DHQ: Dakarun Sojoji Sun Hallaka Ƴan Ta'adda Sama da 900, Sun Kama Wasu Masu Yawa a Najeriya

DHQ: Dakarun Sojoji Sun Hallaka Ƴan Ta'adda Sama da 900, Sun Kama Wasu Masu Yawa a Najeriya

  • Sojojin Najeriya sun samu nasarar halaka ƴan ta'adda sama da 900, sun kana wasu 621 a sassa daban-daban na kasar nan a watan Fabrairu
  • Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ce ta bayyana haka yayin da take zayyana nasarorin rundunar soji a tsawon wata ɗaya ranar Alhamis
  • Manjo Janar Edward Buba, mai magana da yawun DHQ ya ce dakarun sun kwato tulin makamai tare da ceto mutanen da aka yi garkuwa da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Hedkwatar tsaron Najeriya (DHQ) ta bayyana cewa dakarun rundunar sojoji sun samu nasarar kawar da ƴan ta'adda akalla 974 daga doron duniya a wata ɗaya.

DHQ ta ce jami'an sojin sun kuma cafke ƴan ta'adda 621 tare da ceto mutane 466 da aka yi garkuwa da su a samame daban-daban da suka kai a sassan ƙasar nan a watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda, sun ceto mutanen da suka sace

Dakarun sojin Najeriya.
Sojoji Sun Kashe Yan Ta'adda 974, Sun Kama Wasu Da Yawa a Wata 1, In Ji DHQ Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Twitter

Mai magana da yawun hedkwatar tsaro, Manjo Janar Edward Buba ne ya bayana haka yayin da yake bayanin nasararon da sojoji suka samu cikin wata ɗaya a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane irin makamai sojoji suka kwato?

Buba ya ce sojojin sun kwato makamai kala daban-daban 1,573, bindigu ƙira daban-daban 23,345 da alburusai masu yawa a cikin watan, Daily Trust ta rahoto.

Ya lissafa makaman da aka kwato da suka hada da bindigogi kirar AK47 guda 640, bindigogi na gida guda 248, bindigogin fanfu 93, da wasu bindigogi 168.

Ya ce sojojin sun kuma kwato lita miliyan 8.9 na danyen mai da aka sace, lita miliyan 1.06 na AGO da aka tace ba bisa ka'ida ba, lita 18,950 na DPK da lita 45,950 na fetur da dai sauransu.

Ƴan ta'adda sun miƙa wuya

A Arewa maso Gabas, Buba ya ce dakarun Operation Hadin Kai sun kashe ‘yan ta’adda 242, sun kama 57, tare da kubutar da mutane 42 da aka yi garkuwa da su.

Kara karanta wannan

Sabon gwamnan CBN da tawagarsa ne suka jefa ƴan Najeriya cikin tsadar rayuwa? Gaskiya ta fito

Buba ya ce mayakan Boko Haram/ISWAP 1,157 da iyalansu sun mika wuya ga sojoji a cikin wata ɗaya, kamar yadda Guardian ta tattaro.

Jama'a sun fara zanga-zanga kan tsaro

A wani rahoton na daban Jami'an tsaro sun tarwatsa wasu fusatattun mutane da suka toshe babban titin Kaduna zuwa Abuja da sunan zanga-zanga.

A safiyar Alhamis, 29 ga watan Fabrairu, ne mutanen garin Gonin Gora a karamar hukumar Chikun, suka mamaye titin saboda harin da 'yan bindiga suka kai masu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262