Adamawa: An Garkame Direba a Kan Laifin Kwankwade Bokiti 5 Na Burkutu
- Wani diraba ya gamu da fushin kotu a jihar Adamawa bayan da ta same shi da laifin kwankwade bokiti biyar na barasa a Yola
- Ba shanye barasar ne ya jefa direban a matsala ba, jami'i mai shigar da ƙara ya ce Donald ya yi yunƙurin tserewa don kar ya biya kudin giyar
- Yunkurin tsere ba tare da biyan kudin barasa da kifin da direban ya ci ba, ya saba wa sashi na 302 na kundin aikata laifuffuka a cewar jami'in
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Yola, jihar Adamawa - Wata kotu a Yola, jihar Adamawa ta garkame wani direba David Donald a gidan yari bisa zargin ya damfari wata mata sama da bokiti biyar na giyar 'burkutu'.
Daily Trust ta ruwaito wanda ake karar dan karamar hukumar Karim Lamido a jihar Taraba, ya amsa laifinsa na satar kayan wanda ya saba wa sashi na 302 na kundin laifuffuka.
Direban ya yi yunkurin tserewa bayan shan barasar
Dan sanda mai shigar da kara, Sajan Kabiru Abubakar, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhumar ya aikata laifin ne a Yola a ranar Yola a ranar 21 ga watan Fabrairun 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sajan Abubakar ya ce Donald ya karbi bukiti biyar na burkutu da faranti biyu na miyar kifi a shagon matar wanda kudin da ya kai naira 6,600, amma ya ki biya kuma ya yi yunkurin tserewa.
Ya ce Felicity Sunday da Linda Ali, ne suka kai karar mutumin ga ‘yan sanda, inda suka zargi Donald da kin biyan kudadensu da kuma yunkurin tserewa, rahoton shafin Linda Ikeji.
Asali: Legit.ng