"Komai Daidai": An Cika da Murna Yayin da Aka Daina Dauke Wutar Lantarki a Wani Birni a Najeriya
- Kamfanin samar da wutar lantarki na Geometric ya samar da wutar lantarki na sa’o’i 48 ba tare da katsewa ba ga mazauna garin Aba da ke jihar Abia
- Tsawon sa'o'i 48 da aka samu na wutar lantarki ba tare da katsewa ba ya haifar da gagarumar murna daga mazauna birnin waɗanda ba za su iya ɓoye farin cikin su ba
- An ƙaddamar da tashar wutar lantarkin ne shekaru 20 bayan fara aikinta a ƙarƙashin tsohon ministan wutar lantarki Barth Nnaji
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Aba, jihar Abia - Mazauna garin Aba, babban birnin kasuwanci a jihar Abia na cikin farin ciki bayan shafe sa'o'i 48 suna samun wutar lantarki ba tare da katsewa ba.
Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, wasu sassan garin Aba na ci gaba da samun wutar lantarki ba tare da katsewa ba.
An dai samu wutar lantarkin ne bayan da aka kunna ɗaya daga cikin na'urorin samar da wutar lantarki guda huɗu a tashar wutar lantarki ta Geometric a ranar Lahadi, 25 ga watan Fabrairun 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yaushe aka ƙaddamar da tashar?
An ƙaddamar da tashar ne shekaru 20 bayan da aka fara aikinta a ƙarƙashin tsohon ministan wutar lantarki, Barth Nnaji.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da tashar samar da wutar lantarkin a ranar Litinin, 26 ga watan Fabrairu.
Gwamna Alex Otti ya ce a yanzu birnin na kasuwanci a shirye yake domin zuwan ƴan kasuwan cikin gida da na ƙasashen waje.
Wani mai amfani da manhajar X, Chude Nnamdi, @chude__, ya sanya bidiyon wata mazauniyar garin tana murnar samun wutar lantarki a kullum a ranar Laraba, 28 ga watan Fabrairu.
A cikin bidiyon, wata mata da ke magana da Turanci da Igbo ta ce:
"Haske ya samu, Aba zuwa duniya. Kwanaki nawa yanzu? Dubi A.C ko'ina ya ɗau raɓa."
Chude ya rubuta cewa:
"Yanzu mazauna Aba suna samun wutar lantarki 24/7. A halin yanzu garin Aba shine birni mafi bunƙasar rayuwa da saka hannun jari a Najeriya. Mulki ba wasa ba ne."
Kamfanin samar da wutar lantarki da ke garin Osisoma, zai samar da wutar lantarki 27/4 ga gidaje da kamfanoni.
Ƙasashen da Aka Fi Ɗauke Wutar Lantarki
A wani labarin kuma, mun tattaro muku jerin ƙasashen nahiyar Afirika waɗanda ba su tsayayyiyar wutar lantarki.
Ƙasashen Najeriya, Nijar da Afirika ta Tsakiya na daga cikin ƙasashen da aka fi ɗauke wutar lantarki a nahiyar Afirika.
Asali: Legit.ng