Wace Ƙasa Ya Fi Arha? Jerin Farashin Litar Man Fetur a Najeriya da Wasu Ƙasashen Afirka
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Matsakaicin farashin man fetur a duniya shi ne Dalar Amurka 1.31 watau kwatankwacin Naira 2,000 kenan a kuɗin Najeriya kan kowace lita ɗaya.
Kamar yadda The Nation da tattaro a wani rahoto ranar Alhamis, 29 ga watan Fabrairu, akan samu banbancin farashin man fetur a wasu ƙasashen.
Farashin yana banbanta ne a ƙasahe saboda dalililai da dama kama daga yadda wasu gwamnatocin ƙasashen ka ware tallafi na musamman a kan fetur domin sauƙaƙawa al'umma.
A nahiyar Afirka, ƙasar Mali tana siyar da man fetur N2,266 kan kowace lita ɗaya yayin a nan gida Najeriya ake siyar da lita ɗaya kan N668.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kan samu irin wannan banbancin farashin ne saboda yanayin harajin ƙasashe da kuma wataƙila tallafin da ake ware wa man fetur.
Kowace ƙasa a duniya tana samun damar siyan fetur a farashi iri ɗaya na kasuwar duniya amma kuma a kan sanya haraji kala daban-daban.
Sakamakon haka ne ake samun banbanci a farashin litar fetur tsakanin ƙasashe kamar yadda kuka gani a ƙasar Mali da kuma Najeriya.
Legit Hausa ta tattaro muku farashin fetur a wasu ƙasashen Afirka a Naira da kuma dalar Amurka.
Jerin farashin litar man fetur a Naira
1. Mali: ₦2,266
2. Ivory Coast: ₦2,289
3. Kamaru: ₦2,196
4. Togo: ₦1,832
5. Benin: ₦1,779
6. Ghana: ₦1,594
7. Najeriya: ₦668
Farashin litar fetur a waɗannan ƙasashe a Dalar Amurka
1. Mali: $1.435
2. Ivory Coast: $1.450
3. Kamaru: $1.391
4 Togo: $1.160
5 Benin: $1.127
6. Ghana: $1.009
7. Najeriya: $0.423
Idna baku manta ba, Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya tuge tallafin man fetur a ranar da aka rantsar da shi a watan Mayu, 2023.
An ƙi karban muƙami a gwamnatin Tinubu
A wani rahoton na daban wanda shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya naɗa a matsayin darakta a babban bankin Najeriya CBN ya ƙi karɓan mukamin.
Sanata Orji Kalu ne ya bayyana haka yayin tantance waɗanda aka naɗa a zauren majalisar dattawa ranar Alhamis, 29 ga watan Fabrairu.
Asali: Legit.ng