Wata Ɗaya Bayan Gwamna Ya Tsige Sarakuna 3, An Zaɓi Sabon Sarki a Jihar PDP

Wata Ɗaya Bayan Gwamna Ya Tsige Sarakuna 3, An Zaɓi Sabon Sarki a Jihar PDP

  • Kimanin kwanaki 30 bayan Gwamna Adeleke ya tsige sarakuna 3, an zaɓi sabon sarkin Iree, ɗaya daga cikin masarautun uku a jihar Osun
  • Yarima Ibraheem Oyelakin ne ya samu nasarar zama sabon Oba na Iree da ke ƙaramar hukumar Boripe bayan bin matakan da ya dace
  • A wata sanarwa da sabon basaraken ya fitar, ya buƙaci sauran ƴan takara su ba shi haɗin kai domin tafiyar da mulki cikin nasara

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Osun - Yarima Ibraheem Oyelakin ya samu nasarar zama sabon zaɓaɓɓen Sarkin masarautar Iree a jihar Osun da ke Kudu maso Yammacin Najeriya.

Wannan na zuwa ne kimanin wata ɗaya bayan Gwamna Ademola Adeleke na jihar ya tsige sarakuna uku daga kan karagar mulki.

Kara karanta wannan

Mataimakin gwamna ya ƙara tada rigima, ya dira sakateriyar PDP ta ƙasa kan muhimmin abu 1

Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun.
Wata Daya Bayan Gwamna Adeleke Ya Tsige Sarakuna 3, An Zabi Sabon Sarki a Osun Hoto: Ademola Adeleke
Asali: Facebook

Jaridar The Naton ta tattaro cewa Gwamna Adeleke ya tsige Owa na Igbajo, Oba Adegboyega Famodun, Are na Iree, Oba Ademola Ponle, da Akirun na Ikirun, Oba Yinusa Akadiri, saboda kura-kuran da aka yi wajen zabensu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka nan kuma gwamnan na PDP ya ba da umarnin a sake sabon sale kuma a bi matakai domin zaɓo sabbin sarakunan waɗannan masarautu guda uku.

Wa aka zaɓa a matsayin sabon sarkin Iree?

Yarima Ibraheem Oyelakin daga gidan sarautar Oyekun ya samu nasarar zama zaɓaɓɓen Oba na masarautar Iree da ke yankin ƙaramar hukumar Boripe a jihar Osun.

A wata sanarwa da zababben Oba ya fitar, Yarima Ibraheem Oyelakin ya miƙa godiyarsa ga sauran ƴan takara tare da neman goyon bayansu a mulkinsa.

A kalamansa ya ce:

"Ba zan yi wasa da wannan gatan da kuka mun ba, Ina ƙara godewa Iwarefa mefa na Iree, majalisar sarakunan Aree, Yarima da Gimbiya, Asiwaju na Iree, shugaban IPA na kasa da sauran su bisa goyon bayan da suka ba ni.

Kara karanta wannan

Sabon gwamnan CBN da tawagarsa ne suka jefa ƴan Najeriya cikin tsadar rayuwa? Gaskiya ta fito

"Ni'imar da muka roƙa ta sauko, kyakkyawan labari da muke jira ya ƙariso, abin da ya rage mu ɓinne dukkan abubuwan da suka wuce kama daga saɓani, mafarkai da tunani.
"Alaƙar da ta haɗa mu ta fi ƙarfin dukkan saɓanin da ke neman watsa mu, kowa ya san Iree masarauta ce mai cike da zaman lafiya, mu haɗu mu dawo da wannan tarihi."

Wane abu ya kai Tinubu jihar Ondo?

Wani rahoto ya nuna cewa Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci mai martaba basaraken Owo, Oba Ajibade Gbadegesin Ogunoye, domin yi masa ta'aziyyar rasuwar Akeredolu.

Shugaban ƙasar ya bayyana tsohon gwamnan a matsayin mayaƙi mara tsoro wanda zai yi wahala a iya cike giɓin da ya bari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262