EFCC: Manyan Kwastam Sun Yi Dumu-Dumu Cikin Badakalar Cin Hancin Biliyoyin Kudi
- An samu hujjoji da ke nuna wasu manyan jami’an kwastam sun yi kudi ta hanyar karbar cin hanci a iyakokin Najeriya
- Ma’aikatan kwastam da aka ba amanar iyakoki su kan karbi biliyoyi daga hannun masu fasa kauri a ‘yan shekarun nan
- Hukumar EFCC ta cafke wadanda ake zargi da wannan aiki na assha, amma a karshe kusan babu abin da aka iya yi
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Wani rahoto da aka bankado ya nuna yadda ake zargin yin rufa-rufa domin birne rashin gaskiyar da aka tafka a hukumar kwastam.
Premium Times ta rahoto cewa ana zargin manyan jami’an kwastam kusan 40 suna da hannu a wata badakalar da ‘yan EFCC su ke bincike.
EFCC ta tono cin hancin da ake yi a kwastam
Ana zargin ma’aikatan hukumar kwastam da karbar cin hanci a hannun ‘yan fasa kauri wajen shigowa ko ficewa da kaya a sace ta iyakoki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
EFCC ta kama akalla bakwai daga cikin ma’aikatan, aka tsare su a shekarar bara bayan gano suna da hannu a badakalar cin hancin N12bn.
Majiya ta ce an samu jami’an hukumar ta kwastam da ake zargi da mallakar gidajen da sun fi karfin samunsu, hakan ya jawo alamar tambaya.
EFCC: An kama wasu jami'ai amma a banza
Daga cikin jami’an da ake magana, rahoton ya ce akwai wanda aka samu da tsabar kudi; $31, 200 da N500, 000 a lokacin da aka cafke shi.
Da aka bincika, sai aka gano cin hancin N1.1bn da ‘yan fasa kauri suka biya ya shigo hannunsa, ana zargin har ya fara maida wasu N250m.
Hadimin shi kuwa sai da ya maida N12m daga cikin N126m da EFCC ta gano a hannunsa.
Cin hancin N9.5bn a gidan kwastam
Akwai jami’in da ke shiyyar Fatakwal da EFCC ta ci karo da N9.5bn da ake zargin ya karba a matsayin cin hanci tun daga 2015 zuwa 2023.
Dole ma’aikacin ya maido N50m kuma ya sha alwashin zai dawo da N800m a nan gaba.
Da bincike ya yi bincike akwai wanda aka samu da N950m, bayan ya shiga hannu EFCC tayi nasarar karbe N583m kafin sauran su fito.
Akwai jami’ai biyu da aka kawo sun samu fiye da N160m a yankin Jibiya kamar yadda aka ce wani ya samu N120m daga cin hanci.
Duk da hukumar yaki da rashin gaskiyar ta kama su, jaridar ta ce ba a iya gurfanar da su a kotu ba, a karshe jami’an sun koma ofis,
An nemi jin ta bakin kwastam da EFCC game da binciken, amma ba a samu komai ba.
Zanga-zangar NLC ta zo karshe
Idan aka yi abubuwan da NLC take so, ana da labari cewa kungiyar ma’aikatan kasar ta ce za a samu saukin kuncin rayuwa a Najeriya.
A yayin janye zanga-zanga, kungiyar NLC ta fadawa Bola Tinubu a shigo da abinci da siminti da sauran kayayaki daga kasashen waje.
Asali: Legit.ng