Tashin Hankali Yayin Wata Sabuwar Cuta Ta Kashe Dalibai 20 a Jihar Arewa, Bayanai Sun Fito
- An samu ɓullar cutar sanƙarau a wasu makarantu da ke ƙaramar hukumar Potiskum ta jihar Yobe
- Cutar wacce ta ɓulla ɗai ta yi sanadiyyar rasuwar ɗalibai 20 a wasu makarantun kwana da ke ƙaramar hukumar Potiskum
- Gwamnan jihar Mai Mala Buni ya umurci ma'aikatar ilmi ta jihar da ta koma ƙaramar hukumar na wani ɗan lokaci domin daƙile ɓarkewar cutar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Yobe - Aƙalla dalibai 20 na wasu makarantun gwamnati na kwana a ƙananan hukumomin Potiskum, Fika, da Fune a jihar Yobe sun rasu sakamakon kamuwa da cutar sanƙarau.
An tattaro cewa an samu mutuwar ɗaliban ne a Kwalejin Kimiyyar Fasaha ta Gwamnati, Kwalejin Kimiyyar Fasaha ta Mata ta Gwamnati, da Kwalejin Mata ta Gwamnatin Tarayya, duk a ƙaramar hukumar Potiskum.
Wata majiya a garin ta shaida wa jaridar Daily Trust cewa aƙalla ɗalibai 20 ne suka mutu, inda ta ƙara da cewa yawancin ɗaliban da abin ya shafa an kwantar da su a asibitin kwararru da ke Potiskum inda suke karɓar magani.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me hukumomi suka ce kan lamarin?
Da aka tuntuɓi kwamishinan ilimi na farko da sakandire, Dr. Muhammad Sani Idris, ya tabbatar da ɓullar cutar, inda ya ce cutar wacce ake zargin sanƙarau ce ta kashe ɗalibai 20.
Ya ce gwamna Mai Mala Buni ya umurci ma’aikatar ilimi ta jihar da ta koma Potiskum na wani ɗan lokaci domin daƙile ɓarkewar cutar.
Kwamishinan ya kuma tabbatar da cewa an kwantar da ɗalibai da dama a asibitin ƙwararru na Potiskum.
An Samu Gobara a Dakin Kwanan Dalibai a Yobe
A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu tashin wata mummunar gobara a ɗakin kwanan ɗalibai mata na jami'ar jihar Yobe.
Gobarar wacce ba a san musabbabin tashinta ba dai ta shafi ɗakin kwanan ɗalibai wanda yake ɗauke da sama da ɗalibai 150.
Gwamna Mai Mala Buni na jihar ya jajantawa mahukuntan jami'ar da ɗalibai kan tashin gobarar inda ya umurci da a gaggauta kai musu kayan agaji.
Asali: Legit.ng