Hukumar NDLEA Ta Yi Kamu Mafi Girma a Tarihinta, Bayanai Sun Fito

Hukumar NDLEA Ta Yi Kamu Mafi Girma a Tarihinta, Bayanai Sun Fito

  • Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta kama aƙalla masu safarar miyagun ƙwayoyi guda huɗu a jihar Legas
  • Jami’an hukumar NDLEA sun kama waɗanda ake zargin ne a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke jihar Legas
  • An tattaro cewa cafke kayan mayen da aka yi shi ne mafi girma da hukumar ta taɓa yi a tarihinta

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Ikeja, Legas - Hukumar NDLEA ta sanar da samun nasarar tarwatsa wata ƙungiyar masu aikata laifuka da ta ƙware wajen safarar kayan maye a ƙasashe da dama.

Bayan wani samame na kwanaki 12 da suka yi, sun cafke mambobin ƙungiyar tare da ƙwace kayen maye mafi girma a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas.

Kara karanta wannan

Obasanjo ya yi sabuwar fallasa kan adadin man fetur din da ake sacewa a Najeriya

NDLEA ta cafke kwayoyi a Legas
Hukumar NDLEA na neman mutum 11 cikin 'yan kungiyar Hoto: NDLEA
Asali: Twitter

Shugaban hukumar ta NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (Mai Ritaya) ne ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai a Legas, inda ya jaddada ƙudirin hukumar na tabbatar da gaskiya wajen yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Su wanene ƴan ƙungiyar?

A cewar Marwa:

"Wannan ƙungiyar na da faɗi sosai a Najeriya, domin kayayyakin da muka kama suna ɗauke da sunaye da dama, wanda ke nuna cewa kayan na ƴan ƙungiyar ne daban-daban.
"Bugu da ƙari kuma, a binciken da muka yi, mun bankaɗo jerin sunayen masu karɓar haramtattun ƙwayoyi daga wanda ake zargin, a karshe mun samu nasarar zaƙulo shugaban ƙungiyar a nan Najeriya, Reginald Peter Chidiebere.
"Binciken da muka yi ya nuna cewa ya mallaki Otal din Golden Platinum and Suite, wanda ke lamba 16 titin Reginald Peter Chidiebere, Hope Estate, Ago Palace."

Kara karanta wannan

APC ta shiga matsala yayin da dan takarar gwamna ya yi barazanar daukar mataki 1 a kanta

NDLEA na neman mutum 11, ta kulle asusun banki 107

Ya yi ƙarin haske da cewa matakan da aka ɗauka kan mutanen da ke da hannu a cikin ƙungiyar sun haɗa da dakatar da asusun banki 107 mallakin mambobin ƙungiyar 14 da kuma gano N119,582,928.31 a wasu asusun banki.

Ya bayyana cewa an keɓe otal da wani gidan da ke da alaƙa da shugaban ƙungiyar a Najeriya, Reginald Peter Chidiebere, da kuma wani gidan da ke da alaƙa da shugaban ƙungiyar a Mozambique, Festus Ibewuike, da ke yankin Ago Palace, domin gwamnatin tarayya ta kwace.

Ya bayyana cewa matakin ya haifar da ƙarin nasara a ranar 22 ga watan Fabrairu, lokacin da aka kama Misis Confidence Ndidiamaka, wata mata ƴar ƙungiyar kuma matar Festus Ibewuike, a yankin Ago Palace.

NDLEA Ta Magantu Ƙan Ɗaukar Aiki

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar NDLEA ta ja hankalin mutane kan ayyukan ƴan damfara masu cewa ta fara ɗaukar aiki.

Hukumar ta buƙaci mutane da su yo hattara kada su faɗa hannun miyagu masu jiran ƴar dama kaɗan su tafka musu ɓarna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng