Jami'an Tsaro Sun Dira Kan Ƴan Bindiga, Sun Kashe Da Yawa Sun Ceto Mutum 40 a Arewa

Jami'an Tsaro Sun Dira Kan Ƴan Bindiga, Sun Kashe Da Yawa Sun Ceto Mutum 40 a Arewa

  • Yan sanda da taimakon mafarauta sun yi nasarar halaka ƴan bindiga masu yawa tare da ceto mutane 40 da aka yi garkuwa da su a Taraba
  • Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP David Iloyanomon, ya ce jami'an tsaro sun ragargaji ƴan bindiga, sun kamo 10 daga cikinsu
  • Ya ce haɗin guiwa tsakanin ƴan sanda da mafarauta tana haifar da ɗa mai ido kuma zasu ƙara karfafa wannan alaƙa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Taraba - Kwamishinan ‘yan sandan jihar Taraba, David Iloyanomon, ya ce jami’an ‘yan sanda da mafarauta sun ceto mutane 40 da aka yi garkuwa da su a jihar.

CP Ya bayyana cewa jami'an sun kubutar da mutanen ne daga hannun ƴan bindiga masu garkuwa da mutane a saman tsaunuka a kananan hukumomin Yorro da Zing na jihar Taraba.

Kara karanta wannan

Yan sanda da sojoji sun yi kazamin artabu da ƴan bindiga, sun samu nasara a jihar Arewa

Yan sandan Najeriya.
Jami'an tsaro sun kubutar da mutane 40 da aka yi garkuwa da su a Taraba Hoto: PoliceNG
Asali: Twitter

Kwamishinan ‘yan sandan ya faɗi haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Jalingo, babban birnin jihar ranar Litinin, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake faɗin yadda aka samu wannan nasarar, kwamishinan ƴan sanda ya ce an ceto mutanen ne sakamakon haɗa kai da mafarautan yankin, waɗanda sun san ciki da wajen jejin.

Ya ce:

"Mun fara amfani da wasu dabaru kamar haɗa kai da mafarauta da ƴan banga, mun yi nasarar fatattakar su tare ɗa halala da yawa daga cikin ƴan bindigar."

Wace nasara aka samu bayan ceto mutum 10?

Kwamishinan ya kuma bayyana cewa dakarun sun kama masu garkuwa da mutane 10 a lokacin da suke kokarin tserewa daga maboyarsu a kan dutsen.

Iloyanomon ya ce tuni aka kai wadanda aka ceto zuwa asibitin ‘yan sanda da ke Jalingo, babban birnin jihar Taraba domin yi musu magani.

Kara karanta wannan

'Yan sanda da dakarun sojoji sun yi wa ƴan bindiga rubdugu, sun samu gagarumar nasara a Arewa

A cewarsa, da zaran kwararrun likitoci sun tabbatar da lafiyarsu za a sake maida su cikin iyalansu.

Ya ce rundunar ‘yan sandan za ta ƙarfafa hadin gwiwa da mafarauta da ’yan banga wajen yaki da ‘yan bindiga a jihar, kamar yadda Tribune Online eta rahoto.

Yan sanda da sojoji sun farwa yan bindiga a Katsina?

A wani rahoton kun ji cewa Ƴan sanda da sojoji sun nuna wa ƴan bindiga banbanci, sun fatattake su tare da ceto mutum 10 da suka yi yunƙurin garkuwa da su a Katsina.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, Abubakar Aliyu, ya ce jami'an tsaro sun samu wannan nasara ne ranar Lahadi da ta gabata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262