CJN Ariwoola Ya Rantsar da Sabbin Alkalan Kotun Koli, Ya Ba Su Shawara Mai Ratsa Jiki

CJN Ariwoola Ya Rantsar da Sabbin Alkalan Kotun Koli, Ya Ba Su Shawara Mai Ratsa Jiki

  • Alƙalan alƙalan Najeriya ya rantsar da sabbin alƙalan Kotun Ƙoli guda 11 a ranar Litinin, 26 ga watan Fabrairu
  • CJN Ariwoola ya buƙaci alƙalan da su gudanar da ayyukansu bisa tsoron Allah domin sauke nauyin dake kansu
  • Alƙalin Alƙalan ya tunatar da su cewa akwai ranar da za su bayyana a gaban Allah domin yin bayani kan hukuncin da suka yanke

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Babban alƙalin alƙalan Najeriya, Mai shari’a Olukayode Ariwoola, ya buƙaci sabbin alƙalan Kotun Ƙoli da su rika ganin kansu a matsayin wakilan Allah a duniya.

A cewarsa, duk wani hukunci da alƙalan suka yanke, za a iya sauya shi ne kawai idan anje lahira, cewar rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Dan takarar shugaban kasa ya bayyana yadda manufofin Tinubu suka jawo wahala a Najeriya

Ariwoola ya ba alkalan Kotun Koli shawara
CJN Ariwoola ya bukaci alkalan su yi adalci Hoto: Dr. Francis
Asali: UGC

Ariwoola yayi magana ne a Abuja jim kaɗan bayan rantsar da sabbin alƙalan Kotun Ƙoli guda 11, a ranar Litinin, 26 ga watan Fabrairun 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wacce shawara CJN Ariwoola ya ba alƙalan?

Ya kuma buƙaci alƙalan da su kasance cikin shiri don suka ko cin zarafi daga masu ƙarar da suka yi rashin nasara a ƙararrakinsu, rahoton Daily Trust ya tabbatar.

Ya ƙara da cewa a matsayin masu shari’a na kotun ƙarshe na ƙasa, tsammanin masu ɗaukaka ƙara a kansu yana da matuƙar yawa sosai.

A kalamansa:

"Ku dubi kanku a matsayin wakilan Allah a duniya, domin kowane hukunci da aka yi a wannan matakin ba a iya sauya shi sai a lahira kawai.
"Ba yadda za a yi ka faranta wa ɗan Adam rai, musamman masu ƙara. Hanya mafi sauki don gazawa a rayuwa ita ce ta ƙoƙarin faranta wa kowa rai.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Masu yi wa kasa hidima (NYSC) sun bukaci a yi musu karin alawus, sun fadi dalili

"Abin bautar da za ku ji tsoro shi ne Allah Maɗaukakin Sarki. Da zarar hukuncinku ya yi daidai da abin da Allah yake so daga gare ku, kuma ya yi daidai da tsarin mulkin ƙasa, to ku ɗauki kanku a matsayin wanda ya fi kowa farin ciki da walwala a duniya."

Ariwoola ya tunatar da alƙalan cewa wata rana za su bayar da bayanin yadda suka tafiyar da aikinsu a matsayin alƙalai a gaban Allah.

Dalilin Tsaiko Wajen Rantsar da Alkalai

A wani labarin kuma, kun ji cewa an bayyana dalilan da suka sanya aka samu tsaiko wajen rantsar da sabbin alƙalan Kotun Ƙoli.

Wasu daga cikin dalilan da suka jawo tsaiko wajen rantsar da alƙalan sun haɗa da rashin wurin zama da kayayakin sufuri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng