Babban Labari: Tinubu Ya Shirya Amfani da Rahoton Oronsaye, Zai Yi Wani Babban Sauyi a Najeriya
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya shirya amfani da rahoton Stephen Oronsaye na sake fasalin hukumomi da ma'aikatun gwamnati
- Idan Tinubu ya yi amfani da rahoton, hakan na nufin zai rushe wasu hukumomi da ma'aikatu yayin da wasu za a hade su waje ɗaya
- Ministan watsa labarai, Mohammed Idris ya ce wannan matakin zai taimaka wajen rage tsadar tafiyar da mulki a Najeriya, kuma abu ne mai kyau
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya kuduri aniyar aiwatar da rahoton Stephen Oronsaye da ya nemi gwamnati ta hade wasu hukumomi waje daya tare da rushe wasu.
Majalisar zartaswa ta tarayya (FEC), a ranar Litinin, 26 ga watan Fabrairu, ta amince da amfani da rahoton Orosanye, da nufin rage kudaden da gwamnati ke kashewa wajen tafiyar da lamurran kasar.
Shekaru 12 bayan mika rahoton Stephen Oronsaye
Mai magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga ne ya sanar da matakin na shugaban a cikin wani sako a kan shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Onanuga ya yi nuni da cewa Tinubu ya dauki wannan mataki shekaru 12 bayan da Stephen Oronsaye ya mika rahotonsa na yadda za a sake fasalin ma'aikatu da hukumomin gwamnati.
Shi ma ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Idris, ya yi karin haske ga manema labarai jum kadan bayan taron na FEC.
Matakin zai rage tsadar tafiyar da mulki a Najeriya
A cewar Idris, amincewa da rahoton na nufin za a rushe wasu hukumomi da kwamitoci da ma’aikatun gwamnati yayin da za a hade wasu zuwa abu daya.
“Kamar yadda na ce, wannan wani babban mataki ne mai muhimmanci. Matakin zai taimaka wajen kawo daidaito ko sake fasalin ayyukan gwamnati gaba ɗaya
Na biyu, matakin ya yi daidai da manufar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na rage tsadar tafiyar da mulki."
- Inji Idris.
Asali: Legit.ng