Gwamnan APC Ya Kori Shugaban Karamar Hukuma, Ya Maye Gurbinsa Nan Take

Gwamnan APC Ya Kori Shugaban Karamar Hukuma, Ya Maye Gurbinsa Nan Take

  • Gwamnan jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo, ya sanar da korar shugaban riƙon ƙwarya na ƙaramar hukumar Ofu ta jihar
  • Gwamnan ya amince da tsige Honarabul Hassan Atawodi daga muƙaminsa a wata sanarwa da sakatariyar gwamnatin jihar ta fitar a ranar Litinin, 26 ga watan Fabrairu
  • Sanarwar ta kuma umurci Atawodi da ya miƙa dukkanin kadarorin gwamnati da ke hannunsa ga wanda aka naɗa domin ya maye gurbinsa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kogi - Gwamnan jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo, ya amince da tsige Hon. Hassan Atawodi a matsayin shugaban rilo na ƙaramar hukumar Ofu.

Hakazalika Gwamna Ododo ya amince da naɗin Musa Muhammed Lawal a matsayin sabon shugaban riƙon ƙwarya na ƙaramar hukumar Ofu nan take, cewar rahoton jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya rantsar da kwamishinan NPC, ya shiga muhimmin taro da jiga-jigai a Villa

Ododo ya kori shugaban karamar hukuma
Gwamna Ododo ya kori shugaban karamar hukuma kan zargin cin hanci Hoto: @OfficialOAU
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da sakatariyar gwamnatin jihar (SSG), Misis Folashade Ayoade, ta fitar ranar Litinin a Lokoja, babban birnin jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta kuma umurci Hassan Atawodi da ya miƙa dukkan kadarorin gwamnati da ke hannun sa ga sabon shugaban riƙon ƙwaryan.

Ta kuma umurce shi da ya miƙa dukkan al’amuran ƙaramar hukumar ga Lawal cikin gaggawa.

Sakatariyr ta ƙara da cewa tsige shi ya yi daidai da tsarin Gwamna Ododo na rashin amincewa da duk wani nau'i na cin hanci da rashawa a gwamnatinsa.

Kotu ta kori ƙarar da ke ƙalubalantar nasarar Ododo

Legit Hausa ta rahoto cewa kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Kogi, ta kori ƙarar da jam'iyyar APP ta shigar kan zaɓen gwamnan jihar.

Kotun dai ta kori ƙarar ne wacce ta nemi a tsige gwamnan jihar, Ahmed Usman Ododo, wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar na watan Nuwamban 2023.

Kara karanta wannan

An maka gwamnonin Najeriya da Wike kara a gaban kotu kan abu 1

Gwamna Ododo Ya Yi Abun Mamaki

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kogi da aka rantsar, Ahmed Usman Ododo, ya zabi yan majalisarsa da wasu manyan mukamai a ranar farko da ya hau mulki.

Ododo, wanda aka rantsar a matsayin gwamnan jihar Kogi na biyar a ranar Asabar, 27 ga watan Janairu, ya gabatar da sunayen wasu kwamishinoninsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng