Tinubu Ya Kafa Kwamiti Mai Bangarori Uku Na Ba Shi Shawara Kan Tattalin Arziki
- Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya kafa kwamitin da zai ba shi shawari kan tattalin arziki a yau Lahadi 25 ga watan Faburairu
- Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke fuskantar koma-baya a fannin tattalin arziki da ci gaba
- An ruwaito bangarori uku da shugaban kasar ya duba wajen kafa wannan kwamiti da zai fara aiki nan ba da jimawa ba
Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas
FCT, Abuja - A wani bangare na kokarin daidaita tattalin arzikin Najeriya, a yammacin Lahadi shugaban kasa Bola Tinubu ya kafa kwamitin ba da shawara kan tattalin arziki mai bangarori uku.
Tsohon shugaban kasa ya ce sun batawa yan Najeriya lokaci, ya fadi tsarin mulkin da ya dace da kasar
Kwamitin, wanda aka kirkira a taron da ya yi da masu ruwa da tsaki a fadar gwamnatin kasar, ya kunshi wakilai daga tarayya, jihohi da kuma kungiyoyi masu zaman kansu, The Nation ta ruwaito.
Da yake jawabi a wurin taron, Tinubu ya ce manufar kafa kwamitin ba komai bane face samar da "karin hobbasa" wajen daidaita tattalin arziki da kuma tabbatar da "mafi kyawun makomar tattalin arziki" ga 'yan Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayanin Tinubu kan tattalin arzikin Najeriya
Jaridar Vanguard ta ruwaito Bola Tinubu na cewa:
"Za mu yi duba ga abin da muke yi mai kyau da wanda muke tafka kuskure domin farfado da tattalin arziki.
"Kamar yadda nake fadi sau tari, mutanen kasar nan ne kadai ya kamata mu biya wa bukata. Kuma mun damu ainun daga kan dalibai har zuwa kan iyaye mata da maza, manoma, 'yan kasuwa kuma mun gane kowa na tare damu a halin da ake ciki."
Ya kuma bayyana cewa, yana kokarin tabbatar da an fitar da 'yan Najeriya daga halin da suke ciki, kuma tabbas zai yi mai yiwuwa wajen farfado da tattalin arzikin kasar.
Faduwar darajar Naira ta taba tattalin arzikin Dangote
A wani labarin, kun ji yadda dukiyar Dangote ta ragu sakamakon ci baya da aka samu a tattalin arzikin Najeriya.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da darajar Naira ke kara lalacewa idan aka kwatanta da dalar Amurka a 'yan kwanakin nan.
An kuma ruwaito yadda Dangote ya rasa matsayinsa na baya a jerin attajiran duniya bayan samun ci gaban Naira.
Asali: Legit.ng