Gobara Ta Tashi a Gidan Karamar Ministan Birnin Tarayya Abuja
- Bayanai sun fito dangane da gobara da ta tashi a gidan karamar ministan babban birnin tarayya, Abuja, Mariya Mahmoud
- Gobarar ta tashi ne a ranar Lahadi, 25 ga watan Fabrairu, a yayin da aka rahoto cewa masu kawo dauki ba su iso da wuri ba
- Legit Hausa ta rahoto cewa hadimin ministan ya tabbatar da afkuwar lamarin, yana mai cewa ana bincike game da musababbin tashin gobarar
Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe
FCT, Abuja - An samu tashin babban gobara a gidan karamar ministan babban birnin tarayya (FCT) Abuja, Dakta Mariya Mahmoud a ranar Lahadi.
Daily Trust ta rahoto cewa gobarar ta fara tashi ne a gidan da ke unguwar Asokoro da ke Abuja da rana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ma'aikatan Hukumar Kashe Gobara ba su samu daman zuwa wurin da wuri a, hakan yasa abin ya kara muni.
Abin da hadimin ministan Abuja ya ce kan gobarar?
Duk da cewa babu wani rahoto a hukumance dangane da afkuwar lamarin, hadimin ministan, Mista Austine Elemue ya tabbatar da afkuwar lamarin amma bai zurfafa bayani ba.
Ya ce ana bincike don gano musababbin gobarar.
Elemue ya ce masu kawo dauki na farko ba su iya ceto komai daga gidan ba.
Kalamarsa:
"Eh, gobara ta tashi a gidan karamar minista. Ana kan bincike domin gano abin da ya yi sanadin gobarar.
"Amma ana zargin matsalar wutar lantarki ne, sai dai za mu jira sakamakon binciken. Babu wanda ya rasa ransa amma ba a iya ceto wani abu daga gidan ba."
Hukumar Kashe Gobara ta Abuja ta yi martani
Da ya ke martani kan gobarar, Amiola Adebayo, mukadashin direktan hukumar kashe gobara na Abuja, ya ce gobarar ta kone komai a bene na farko na gidan.
Adebayo ya ce:
"Da isar mu wurin, mun tarar da cewa bene na farko da sauran na saman duk wuta ya mamaye su.
"Don haka abin da kawai za mu iya yi shine hana wutan ya yadu zuwa kasa, da kuma gine-ginen da ke gefen gidan. Babu rai da aka rasa."
Mummunar Gobara Ta Lakume Shaguna 7 da Dukiyar N25m a Babbar Kasuwar Cross Rivers
A wani rahoton kun ji cewa iftila’in gobara ta cinye wani bangaren babbar kasuwar Watt da ke tsakiyar birnin Calabar a cikin jihar Cross Rivers.
‘Yan kasuwar sun zargi wayoyin wuta da ke rataye a mafi yawan fola-folai da ke tsagaye da kasuwar ne dalilin jawo gabarar.
Asali: Legit.ng