Tsadar Rayuwa: Babangida ya gargadi Tinubu kan yiwuwar juyin mulkin soja a Najeriya? Gaskiya ya fito

Tsadar Rayuwa: Babangida ya gargadi Tinubu kan yiwuwar juyin mulkin soja a Najeriya? Gaskiya ya fito

  • Rade-radin cewa Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) ya gargadi Shugaba Tinubu game da juyin mulki ba gaskiya
  • Sai dai, akwai shafukan sada zumunta na kwaikwayo mai dauke sunan tsohon shugaban mulkin sojin da ke yada batun juyin mulkin
  • Da yawa daga cikin masu bibiyar shafukan na kwaikwayo basu duba don bambance ko shafin da gaske na tsohon shugaban ba ne

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

Minna, Niger - Shugaba Bola Tinubu na shan suka game da matsin tattalin arziki da aka shiga tun bayan da sanar da matakin cire tallafin mai da karya darajar naira.

Matakan da shugaban ya dauka tun bayan rantsar da shi sun janyo hauhawar farashin kayayyaki abinci da sauran bukatun yau da kullum, kuma masu ruwa da tsaki, ciki har da 'yan adawa da shugabannin kwadago, suna ta kira kan janye matakan.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Matasa a Borno sun yi barazanar shiga Boko Haram, bayanai sun fito

Da gaske Babangida ya gargadi Tinubu kan yiwuwar juyin mulki?
Binciken gano gaskiya ya nuna cewa Ibrahim Badamasi Babangida bai gargadi Tinubu kan yiwuwar juyin mulki ba. Hoto: Getty Images
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sannan, an yi zanga-zanga a wasu jihohi a kasar saboda tsadar rayuwa. Jihohin da aka yi zanga-zanga sun hada da Oyo, Cross Rivers, Niger da Kano.

Tsadar rayuwa: Yan Najeriya sun bukaci sojoji su yi juyin mulki

Yan Najeriya da dama sun nuna rashin jin dadinsu a shafukan sada zumunta saboda halin da ake ciki, yayin da wasu ke neman sojoji su yi juyin mulki.

Wani a shafin X (Tuwita), @General_Ibbro (Ibrahim B. Babangida), ya sha bayyana ra'ayinsa kan yiwuwar cewa sojoji za su yi juyin mulki ga gwamnatin Tinubu.

Ga abin da ya rubuta:

"Ba na goyon bayan juyin mulki, amma ina kira ga gwamnatin tarayya da ta dubi halin da 'yan kasar ke ciki, su kawo dauki kafin abin ya zama annoba."

Wani shafin YouTube ya yayata maganar bayan fadar ta a wani shiri, in da ta bayyana maganar a matsayin abin da Babangida ya ce.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi zancen mayar da tallafi da soke karya naira saboda shiga kuncin rayuwa

Gaskiyar batun juyin mulkin Babangida

Babu wata alama da ke nuna cewa tsohon shugaban mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), da ya mulki Najeriya daga 1985 zuwa 1993 ne ya fadi maganar.

Kuma, shafin X din ya fi kama da na bogi kuma babu shaidar tsohon shugaban kasar a rubutun.

Sai dai, da yawan 'yan Najeriya da ke martani a rubutun ba su duba ko shafin gaskiya bane, dalilin da ya sa ake tunanin Babangida ne.

Wani bincike ya kuma bayyana cewa a bude shafin a shekarar 2013 kuma ana gudanar da shi daga Minna, babban birnin Jihar Niger, kuma a nan ne gidan Babangida ya ke.

Babangida ya karyata yi wa Tinubu gargadi game da juyin mulki

Sai dai, mai magana da yawun tsohon shugaban kasar, Deyemi Saka, ya karyata batun ya kuma yi kira ga yan Najeriya da su yi watsi da maganar.

Saka ya ce in akwai bukatar yin irin wannan maganar, Babangida zai bi hanyoyin da suka dace don sanar da shugaban kasar amma ba a shafin sada zumunta ba.

Kara karanta wannan

An yi harbe-harbe yayin da 'yan daba suka tare manyan motoci, sun sace kayan abinci a jihar Arewa

Ga wasu rubutun da wancan shafin mai kama da na Babangida ya yi nan kusa:

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164