'Yan Bindiga Sun Kashe Kwamandan 'Yan Sintiri da Mutum 6 a Katsina

'Yan Bindiga Sun Kashe Kwamandan 'Yan Sintiri da Mutum 6 a Katsina

Wani rahoto ya bayyana cewa wasu yan bindiga sun kashe Sanusi Hassan, kwamandan jami'an sanya ido na Katsina a karamar hukumar Kankara da ke jihar.

Abubakar Salihu, wani mazaunin kauyen da ya shaidawa jaridar The Cable ranar Asabar, ya ce yan bindigar sun yi luguden wuta kan jami'an sintirin a kauyen Yar Tepa ranar Juma'a.

Salihu ya ce lokacin harbe-harben, an kashe kwamandan sintirin tare da wasu jami'ai hudu da karin mutanen gari guda biyu.

Ya ce wasu gawurtattun yan bindiga da ba su dade da kafa sansanin a Yar Tepa ba ne suka shirya harin.

"Wadannan su ne manyan yan bindigar da suka addabi mazauna yankin," in ji shi.

Kungiyar kare hakkin dan adam da wayar da kai (IHRAAC), kungiya mai zaman kanta, ta yi Allah wadai da kisan jami'an.

Kara karanta wannan

Bayan jami'an sun kashe shugabannin 'yan bindiga, tsageru sun afkawa mutane a Kaduna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar tayi kira da a gudanar da bincike, kuma ya zama dole a hukunta masu laifi.

''IHRAAC na mika ta'aziyya ga hukumar sintiri tare da jajen mutuwar kwamanda Ustaz Sanusi Hassan da sauran jami'an da suka rasu sakamakon mummunan harin da ya faru," in ji IHRAAC ranar Juma'a.

"Mutuwar Hassan babban gibi ne ba iya ga hukumar sintiri ba har da mutanen Kankara da Katsina gaba daya.

An yi rashin jajirtaccen kwarai

"IHRAAC ta yi Allah wadai da irin ta'addacin da aka aikata wa kwamanda Ustaz Sunusi Hassan da sauran jami'ai, tana kara bayyana damuwarta game da rashin tsaro a jihar Katsina.
Ya kamata ayi gaggawar kawar da ta'addaci da manyan laifuka a jihar
"IHRAAC ta bukaci a yi kwakkwaran bincike kan harin, a kuma gano tare da hukunta masu laifi."

Da aka tuntube shi, Abubakar Aliyu, mai magana da yawun 'yan sandan jihar Katsina, bai bada tabbacin faruwar lamarin ba, amma ya ce zai bincika ya kuma dawo.

Kara karanta wannan

Kano, Kaduna da wasu jihohi 8 a Najeriya da aka fi amfani da intanet inji wani bincike

Ba a samu jin ta bakinsa ba har zuwa kammala hada wannan rahoton.

A Oktoban 2023, Dikko Radda, gwamnan Katsina, ya kirkiri hukumar tsaro ta 'yan sakai a wani mataki na dakile ayyukan 'yan bindiga a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: