Gwamnan PDP Ya Kai Ziyara Ta Musamman Yankuna 2 da Ƴan Bindiga Suka Tafka Ɓarna a Jihar Arewa

Gwamnan PDP Ya Kai Ziyara Ta Musamman Yankuna 2 da Ƴan Bindiga Suka Tafka Ɓarna a Jihar Arewa

  • Gwamna Dauda Lawal ya kai ziyara ta musamman yankunan da ƴan bindiga suka kai hari a kananan hukumomin Zurmi da Birnin Magaji a Zamfara
  • Yayin wannan ziyara, gwamnan ya yi ta'aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu tare da jaddada shirin gwamnati na dawo da zaman lafiya
  • Ya kuma duba ofishin ƴan sanda da maharan suka ƙona, inda ya ce zai tallafa musu domin su gudanar da aikinsu babu tangarɗa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Zamfara - Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya kai ziyara garuruwa 2 da ƴan bindiga suka kai hari a kananaan hukumomin Zurmi da Birnin Magaji.

Tribune Online ta tattaro cewa a makon jiya, ƴan bindiga suka kai munanan hare-hare a kauyen Nassarawan Zurmi da ke karamar hukumar Zurmi da Godel a Birnin Magaji.

Kara karanta wannan

"Ba wanda zai so zama gwamna na shekara 1 kaɗai" Gwamnan APC Ya Shiga Neman Takara a 2024

Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara.
Gwamnan Lawal Ya Ziyarci Yankuna Biyu da Yan Bindiga Suka Kai Hari a Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Asali: Twitter

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ya ce Lawal ya kai ziyara ne domin nuna goyon baya da ta'aziyya ga waɗanda lamarin ya shafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane mataki gwamnan ya ɗauka?

Gwamnan ya tabbatarwa mazauna ƙauyukan cewa gwamnatinsa ta jajirce da nufin lalubo hanyar dawo da zaman lafiiya mai ɗorewa a faɗin jihar Zamfara.

Da yake duba caji ofis da ‘yan bindiga suka kona a Nasarawan Zurmi, Lawal ya tabbatar wa ‘yan sandan a shirye ya ke ya ba su taimakon da ya dace domin su ci gaba da gudanar da ayyukansu ba tare da wata tangarda ba.

A rahoton Daily Nigerian, Lawal ya ce:

"Ina jajanta muku bisa jami'an ƴan sanda biyu da suka rasa rayukansu a harin ƴan bindiga na baya-bayan nan a Nassarawan Zurmi.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya gamu da sabuwar matsala, ASUU zata sa kafar wando ɗaya da FG kan muhimmin abu 1

“Na fahimci yadda wannan lamarin ya kasance mai muni ga duk wanda ya taɓa kuma ina so in tabbatar muku cewa tunanina da addu’o’ina na tare da iyalan jami’an da suka mutu da kuma daukacin al’umma.
"Na yaba da kwazon dakarun sojoji a yaki da ƴan bindiga. Gwamnatina za ta ci gaba da bayar da dukkan goyon baya da taimakon da suka dace ga sojojin. Tare za mu shawo kan wannan ƙalubale."

Gwamnati ta aika da kayan agaji

A ziyarar da gwamnan ya kai ƙauyen Nasarawan Godal da ke karamar hukumar Birnin Magaji, ya tabbatar wa jama’a cewa ya turo da kayan agaji nan take bayan harin.

"Na zo nan ne domin yin ta'aziyya ga iyalan waɗanda abin ya shafa da kuma ƙara jaddada kokarin gwamnati na tabbatar da tsaro da kwanciyar hankalin mutane.

Abiodun ya ɓullo da shirin raba tallafin N5bn

A wani rahoton na daban Dattawa da masu ƙaramin karfi zasu samu shinkafa kyauta yayin da Gwamna Abiodun ya fara yunkirin ragewa talakawa raɗaɗin tsadar rayuwa a Ogun.

Dapo Abiodun ya tabbatar da haka a wata sanarwa kuma ya ce mazauna Ogun zasu sayi shinkafa a kan asalin farashinta kafin tashin dala.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262