Murna Ta Barke Yayin da Gwamnan APC Ya Fara Siyar da Shinkafa Kan Farashi Mai Rahusa Ga Talakawa
- Dattawa da masu ƙaramin karfi zasu samu shinkafa kyauta yayin da Gwamna Abiodun ya fara yunkirin ragewa talakawa raɗaɗin tsadar rayuwa a Ogun
- Dapo Abiodun ya tabbatar da haka a wata sanarwa kuma ya ce mazauna Ogun zasu sayi shinkafa a kan asalin farashinta kafin tashin dala
- Wannan yunƙurin gwamnan na jam'iyyar APC zai ci gaba har zuwa lokacin da za a warware matsalar da ta taso a kasuwar canjin kuɗi
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ogun - Yayin da ake fama da matsin tattalin arziki, gwamnatin jihar Ogun ta siyo tirelolin buhunan shinkafa domin siyarwa talakawan jihar a farashi mai rahusa.
A cewar gwamnatin jihar, ta ɗauki wannan matakin ne ba don komai ba sai don magance hauhawar farashin kayan abinci a Najeriya.
Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ne ya tabbatar da haka a taron masu ruwa da tsaki wanda ya gudana ranar Alhamis, 22 ga watan Fabrairu, 2024 a Abeokuta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A jerin saƙonnin da ya wallafa a manhajar X watau Twitter, Gwamna Abiodun ya ce zai saka tallafi a shinkafa kuma za a siyarwa mutane a farashi mai sauƙi.
Kan wane farashi gwamnan zai siyar da Shinkafa?
Abiodun ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta siyarwa da al'ummar jihar Ogun buhunan shinkafa a kan asalin farashinta gabanin hauhawar da aka samu bayan faɗuwar darajar Naira.
Wannan wani ɓangare ne na tallafin N5bn da Gwamna Abiodun ya lashi takobin sanyawa a tattalin arzikin jihar Ogun domin magance tsadar rayuwar da mutane suka shiga.
A sanarwan da ya wallafa, Abiodun ya ce:
"Domin tabbatar da an yi adalci wajen rabon tallafin, mun yanke bai wa tsofaffi da masu ƙaramin karfi shinkafar a kyauta yayin da saura zasu siya a farashin asali kafin tashin dala.
"Wannan zai bamu damar ci gaba da wannan aiki daga nan har zuwa lokacin da za a warware matsalar dala, yana da kyau kowa ya sani wannan kalubalen na wani ɗan lokaci ne."
Yaushe dala zata faɗi warwas a Najeriya?
A wani rahoton kuma Dapo Abiodun ya tabbatar da cewa nan da wani taƙaitaccen lokaci dala zata rikito ta faɗo ƙasa yayin darajar Naira za ta dawo a Najeriya.
Gwamnan ya bayyana cewa ya samu wannan tabbaci ne a wurin ganawar da gwamnoni suka yi da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Legit.ng