Sabuwar Annoba Ta Kashe Ma’aikatan Lafiya Uku da Marar Lafiya a Asibitin Sojin Najeriya
- Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa akwai wata sabuwar cuta da ta ɓulla a asibitin soji na 44 NARHK da ke Kaduna
- Rundunar ta ce cutar ta kashe ma'aikatan lafiya guda uku tare da majinyacin da ake fargabar shi ne ke dauke da cutar
- Cutar dai ana mata lakabi da VHF, kuma alamominta na zazzabin cizon sauro ne amma ita tana kashe ƙoda da saka zubar jini
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kaduna - Asibitin sojojin Najeriya da ke Kaduna (NARHK) ya tabbatar da mutuwar ma’aikatan lafiya uku da mara lafiya a cikin kwanaki biyu bayan barkewar wata bakuwar cuta.
Rundunar sojin, a cikin wata sanarwar cikin gida mai dauke da kwanan watan 21 ga watan Fabrairu da Premium Times ta gani ta tabbatar da faruwar lamarin.
Sanarwar mai dauke da sa hannun SO Okoigi, birgediya-janar, an gabatar da ita ne ga hedikwatar rundunar sojojin Najeriya da ke Bonny Cantonment, Victory Island, Legas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Okoigi ya ce:
“Sashen bada agajin gaggawa na asibitin 44 NARHK ya shaida mutuwar ma’aikata 3 da majinyaci a cikin sa’o’i 48 da suka gabata yayin da wasu ke cikin mawuyacin hali.
“Ana fargabar cewa sun mutu ne daga cutar zazzabin zubar jini (VHF), bayan kula da wani majinyaci da ake kyautata zaton shi ne yake dauke da cutar."
Rundunar ta ce ana kamanta alamun cutar da zazzabin cizon sauro wanda kuma ke haifar da mutuwar koda, Channels TV ta ruwaito.
Matakan da aka ɗauka zuwa yanzu
Jami’in ya ce an rufe sashin hadarurruka da ba da agajin gaggawa na asibitin saboda a dakile yaduwar kwayoyin cutar kuma an dauki jinin wadanda suka yi cudanya da majinyacin don yin gwaji.
Haka kuma an aika gawar majinyacin zuwa dakin gwaje-gwaje na cibiyar yaki da cututtuka ta Najeriya (NCDC) da ke Kano don yin bincike.
Sanarwar ta kara da cewa, a halin da ake ciki, an gayyaci kwararrun likitocin jihar Kaduna da su taimaka wajen bankado illolin cutar da nufin dakile yaduwarta.
Gwamnati ta dakatar da fitar da iskar gas zuwa kasashen waje
A wani labarin na daban, gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ta dauki matakin karya farashin iskar gas din girki ta hanyar dakatar da fitar da shi zuwa kasashen waje.
A cewar karamin minista albarkatun man fetur, wannan matakin zai sa gas din ya wadata wanda zai karya farashinsa a kasuwannin kasar.
Asali: Legit.ng