Sojoji Sun Sheke Kasurgumin ‘Dan Bindigar da Ya Kitsa Manyan Hare-Hare a Arewa
- Dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar sheke wani kasurgumin 'dan ta'adda da ya addabi al'umma a Arewacin Najeriya
- An sheke Boderi wanda ya kitsa manyan hare-hare da suka hada da na makarantar 'yan mata na Yauri, makarantar sojoji da kuma jami'ar Greenfield
- Sojoji sun kashe Boderi ne tare da wani kasurgumin 'dan bindiga, Bodejo a wani harin kwanton bauna da suka kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura
Dakarun hedkwatar runduna ta 1 sun kashe kasurgumin 'dan bindiga, wanda aka fi sani da Boderi, a wani harin kwanton bauna.
An rahoto cewa Boderi ne ya shirya hare-haren da aka kai makarantar sojojin Najeriya da ke Kaduna, da kuma sace 'yan matan makarantar Yauri da wasu daliban jami'ar Greenfield, Kaduna.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar sojoji, Onyema Nwachukwu ya saki, ya ce dakarun soji sun kashe Boderi ne tare da wani kasurgumin 'dan bindiga, Bodejo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nwachukwu ya ce:
"Majiyoyin leken asiri sun rahoto cewa an kashe kasurgumin 'dan bindiga Boderi wanda ya kaddamar da manyan hare-hare da suka hada da na makarantar mata ta Yauri, jami'ar Greenfield da makarantar sojojin Najeriya tare da wani 'dan ta'adda, Bodejo."
Yadda aka yi arangama tsakanin sojoji da 'yan bindiga
Ya kuma ce 'yan ta'adda sun budewa dakarun soji wuta a yankin Bada-Riyawa a hanyar titin Kaduna zuwa Birnin Gwari, amma sun mayar masu da martani nan take.
Kakakin sojin ya kuma ce a cikin haka ne dakarun suka kashe biyu daga cikin 'yan ta'addan.
Sojojin sun kuma kwato bindigar AK 47 guda daya, harsasai uku na 7.62mm. wayar Techno 1, makullan Hilux da babura guda uku, tabar wiwi, kayan maye da kuma kudi N13,200, rahoton Trust Radio.
Ya kuma bayyana cewa har yanzu dakarun na bibiyar sauran 'yan ta'addan da suka rage a yankin da ke fama da rikicin ta'addanci.
Sojoji sun hallaka 'yan ta'adda da dama
A wani labarin kuma, mun ji cewa sojojin Najeriya sun kashe ƴan ta'adda 254 tare da kame wasu 264 a cikin mako guda yayin samamen da sojojin suka kai a faɗin ƙasar nan.
Daraktan yaɗa labarai na hedikwatar tsaro ta ƙasa (DHQ), Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a ranar Juma’a, 16 ga watan Fabrairun 2024.
Asali: Legit.ng