Gwamnati Ta Dakatar da Fitar da Iskar Gas Din Girki Zuwa Kasashen Waje, Ta Fadi Dalili

Gwamnati Ta Dakatar da Fitar da Iskar Gas Din Girki Zuwa Kasashen Waje, Ta Fadi Dalili

  • A ranar Alhamis, 22 ga watan Fabrairu, gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ta dakatar da fitar da iskar gas din girki zuwa kasashen waje
  • Karamin ministan albarkatun man fetur, Ekperikpe Ekpo ne ya sanar da hakan a wajen wani taron bita na masu ruwa da tsaki a Abuja
  • Ekpo ya ce gwamnati ta dauki wannan matakin ne domin karya farashin iskar gas din tare da sa wa ya wadata a kasuwannin Najeriya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu ta sanar da cewa daga yanzu ta dakatar da fitar da iskar gas din girki zuwa kasashen waje.

Da ta fitar da sanarwar a ranar Alhamis, 22 ga watan Fabrairu, gwamnati ta ce dakatarwar zai taimaka wajen rage tsadar da gas din ya yi tare da wadatar da shi.

Kara karanta wannan

Malamin addini ya fada ma Tinubu abu 1 da ya kamata ayi da mabuyar Boko Haram

Gwamnati ta dakatar da kai iskar gas din girki zuwa kasashen waje
Domin karya farashin iskar gas din ne gwamnati ta dakatar da kai shi kasashen waje, in ji Ekpo.
Asali: Getty Images

Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Ekperikpe Ekpo ne ya bayyana hakan ga manema labarai a taron “bita ga masu ruwa da tsaki,” a Abuja The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taken taron shi ne "Samar da tabbataccen ma'adinan gas na Najeriya don bunkasa tattalin arziki da cigaban kasa."

Kokarin da gwamnati ke yi na karya farashin iskar gas

Da aka tambaye shi ko me gwamnati ta yi na shawo kan tsadar iskar gas, ya ce, ma’aikatar tana tattaunawa da masu ruwa da tsaki don magance matsalar.

Masu ruwa da tsakin sun hada da hukumar kula da man fetur ta Najeriya (Midstream da Downstream) da masu kamfanoni irin su Mobil, Chevron, da Shell.

Ya bayyana cewa, da zarar an daina fitar da iskar gas zuwa kasashen waje, za a samu karin yawan gas din a kasuwannin cikin gida wanda zai rage farashin sha kai tsaye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.