'Yan Bindiga Sun Kwashi Kashinsu a Hannu Yayin da Sojoji Suka Kai Samame Cikin Daji a Jihar Arewa

'Yan Bindiga Sun Kwashi Kashinsu a Hannu Yayin da Sojoji Suka Kai Samame Cikin Daji a Jihar Arewa

  • Sojojin Najeriya sun samu nasarar kashe ɗan bindiga ɗaya, sun fatattaki wasu da dama a dajin Yadi a jihar Kaduna ranar Talata
  • Kakakin rundunar soji, Manjo Janar Onyema Nwachukwu, ya ce sojojin sun samu wannan nasara ne a wani samame da suka kai sansanin ƴan bindiga
  • Ya ce dakarun sojin sun kwato kayan aikin ƴan ta'addan da suka haɗa da bindigu da alburusai da babura da sauransu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Dakarun rundunar sojin Najeriya sun samu nasarar halaka ɗan bindiga ɗaya tare da kakkabe sansanin ɓoyon ƴan ta'adda a jejin Yadi da ke jihar Kaduna.

Sojojin sun samu wannan nasara ne yayin da suka kai wani samamen tsaftace jejin ranar Talata, 20 ga watan Fabrairun, 2024.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya fusata kan kisan babban jigo a APC, ya ba jami'an tsaro muhimmin umarni

Sojoji sun samu nasara kan ƴan bindiga a Kaduna.
Sojojin Najeriya Sun Halaka Ɗan Ta'adda, Sun Lalata Sansani a Dajin Kaduna Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Getty Images

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da rundunar sojin ta wallafa a shafinta na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter ranar Laraba mai ɗauke da sa hannun kakakin rundunar, Onyema Nwachukwu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nwachukwu, manjo janar ya ce yayin samamen, ƴan bindigan sun yi wa dakarun soji kwantan ɓauna amma duk da haka suka maida martani aka yi ɗauki ba daɗi.

Ya ce:

"Yayin samamen sojojin, ƴan ta'adda sun ɗana musu tarkon kwantan ɓauna amma suka maida martanin ruwan wuta. Sojojin sun kashe mutum ɗaya, sauran suka arce da raunuka."

Sojoji sun kwato makamai da kayan aiki

A cewar kakakin rundunar sojojin, dakarun sun yi nasarar kwato bindigu kirar Ak 47 guda biyu, da Ak 47 Magazine da alburusai kala daban-daban.

"Sauran abubuwan da aka kwato sun hada da Babura guda uku, na'urorin samar da wutar lantarki guda biyu, Desert Camouflage guda biyu, takalmin jeji guda biyu, sarkokin kafa da na hannu da ake daure wadanda aka yi garkuwa da su."

Kara karanta wannan

Kwamandojin ƴan ta'adda 3 da wasu mayaƙa 22 sun baƙunci lahira a Borno

Nwachukwu ya ce har kawo yanzu sojoji na kan bin ƴan bindigan da suka tsere domin tsaftace dajin daga ayyukan ta'addanci da wanzar da zaman lafiya.

Kwamandojin ƴan ta'adda 3 sun bakunci lahira

A wani rahoton kuma Jirgin rundunar sojin sama NAF ya halaka manyan kwamandojin ISWAP uku da ƙarin wasu ƴan ta'adda a wani luguden wuta a jihar Borno.

Zagazola Makama ya tattaro cewa jirgin yaƙin ya yi ruwan bama-bamai kan maɓoyar ƴan ta'addan a kauyen Arinna Woje da ke yankin Marte.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262