Akpabio Ya Samu Matsala da 'Yan Najeriya Kan Abu 1 tak
- Kalaman shugaban majalisar dattawa kan zanga-zangar da ake yi a ƙasa ba su yi wa ƴan Najeriya daɗi ba
- Sanata Godswill Akpabio ya yi iƙirarin cewa zanga-zangar da ake yi a sassan ƙasar nan wasu ne ke ɗaukar nauyinta
- Waɗannan kalaman na shugaban majalisar dattawan sun jawo ƴan Najeriya da dama a shafukan sada zumunta sun yi masa martani mai daɗi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya fuskanci kakkausar suka kan cewa ɗaukar nauyin masu zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa aka yi.
Jarridar Daily Trust ta ruwaito cewa, an yi zanga-zanga a sassa daban-daban na ƙasar nan, inda a ranar Litinin ɗin da ta gabata aka yi zanga-zanga a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
Akpabio, yayin da yake magana a zauren majalisar dattawa a ranar Talata, ya ce masu zanga-zangar ba su da masaniya kan ƙoƙarin da majalisar dattawa da gwamnatin tarayya ke yi na shawo kan lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kalamansa:
"Kuna ganin yadda ake ta zanga-zanga a nan da can waɗanda wasu tsiraru suka ɗauki nauyi amma mutanen da suka fito zanga-zangar ba su san komai akai ba.
"Mafi yawan waɗanda aka ɗauki nauyi suka fito zanga-zanga ba su san huɓɓasa da ƙoƙarin da majalisar dattawa da tawagar gwamnatin tarayya ke yi domin daƙile lamarin ba.
Ƴan Najeriya sun caccaki Akpabio
Biyo bayan kalaman na Akpabio dai, ƴan Najeriya sun yi martani mai zafi a shafukan sada zumunta. Ga kaɗan daga ciki a nan ƙasa:
@birastockNFT:
"Ya yi kyau, yanzu cewa yake kenan an ɗauki nauyin zanga-zangar. Ya yi gaskiya. Amma tambaya ta a matsayina na ɗan Najeriya, shin wahala da yunwar da ake fama da su ɗaukar nauyinsu aka yi?
@hungermadra:
“Kana tunanin cewa rayuwa iri ɗaya kake da mutanen da suka zaɓe ka? Kana tunanin za su fahimci abin da kake cewa?
@amudaDewale:
“Ya kamata ƴan majalisa su fito, su shiga mota, su je tashar mota su ji irin abin da ƴan Najeriya ke ji."
@XBrainDennis:
"Bayan Tinubu wannan mutumin shi ne na biyu wanda ya fi ba ƴan Najeriya kunya. Na sanya fata sosai kan shugabancinsa na majalisar dattawa. Amma ni ne wawan da na yi fatan zai yi abin kirki."
Emefiele Ya Yi Barazana Ga Akpabio
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya yi barazanar shigar da ƙara kan Godswill Akpabio.
Emefiele ya yi barazanar ne biyo bayan abin da ya kira ɓata masa suna da shugaban majalisar dattawan ya yi a idon duniya.
Asali: Legit.ng