Mafarauta Sun Kashe Zakin da Ya Yi Sanadin Mutuwar Ma’aikacin Jami’ar OAU
- Mafarauta sun kashe zaki dan shekara 9 da ya yi sanadin mutuwar wani ma’aikacin gidan namun daji, Olabode Olawuyi na jami’ar OAU
- An harbi zakin a kafa yayin da yake cikin kejin sa bayan aikata mummunan al’amarin da ya jefa mutane cikin bakin ciki
- Ma'aikacin mai shekaru 59 da haihuwa ya kasance kwararre a fannin fasahar dabbobi kuma an ce tun zakin na karami ya ke rainonsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Ile-Ife, jihar Osun – An samu karin bayani yayin da mafarauta suka kashe zaki dan shekara 9 da ya kashe wani masanin fasahar dabbobi, Olabode Olawuyi.
Olawuyi ya kasance kwararre ne a fannin fasahar dabbobi ne a jami’ar Obafemi Awolowo (OAU), Ile-Ife, jihar Osun.
Shugaban majalisar dattawa ya tona asirin masu ɗaukar nauyin zanga-zanga kan tsadar rayuwa a jihohi 4
An ruwaito cewa Olawuyi mai shekaru 59 da haihuwa ya kasance yana kula da zakin tun yana dan jariri har zuwa lokacin da ya farmake shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar rahoton BBC Pidgin, bayan afkuwar lamarin, mafarauta suka fara yunkurin kashe zakin.
Legit Hausa ta ruwaito cewa zakin ya kuma raunata wani ma'aikacin da ke aiki a gandun dabbobi na OAU.
Yadda mafarauta suka kashe zaki na OAU
An tattaro cewa mutane da yawa suna tsoron zakin kuma kejin zakin yana da girma da fadi don haka dabban ya sami sararin motsawa cikin walwala.
Mafarautan sun je kusa da kejin suka harbe zakin a kafarsa. Ya yi kokarin guduwa amma ya kasa kamar bayan da harsashi ya same shi.
Sauran mafarauta kuma suna tsaye a waje da bindigogi suna jira idan zakin ya tsere daga kejin ya yi yunkurin kai musu hari.
Yayin da ake yunkurin guduwa, an ruwaito kafar zakin ta karye sakamakon harbin bindigar, inda ya fadi nan take.
Asali: Legit.ng