Farashin Litar Fetur Ya Kai N1,000 a Wajen ’Yan Bumburutu Yayin da Aka Fara Dogon Layi a Gidajen Mai
- A yayin da aka fara wahalar man fetur a jihohin Legas, Abuja da Ogun, 'yan bumburutu sun fara sayar da litar man akan naira 1,000
- A safiyar Laraba, an ga yadda gidajen mai mallakin 'yan kungiyar IPMAN su ke a rufe wanda ya jawo dogon layi a gidajen man NNPC
- Wahalar fetur da ake yi a kasar yanzu ba zai rasa nasaba da gajeren yajin aikin da direbobin dakon mai suka fara ba a ranar Litinin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Masu sayar da fetur a bayan fage da aka fi sani da 'yan bumburutu sun fara sayar da litar fetur akan naira 1,000 a wasu sassa na jihar Legas.
Wannan kuwa ya biyo bayan gajeren yajin aikin da direbobin dakon mai suka shiga wanda ya jawo aka rufe wasu gidajen mai.
Channels TV a ranar Laraba ta ruwaito cewa mafi akasarin gidajen mai mallakin 'yan kasuwa an garkame su da kwaɗo a Legas da Ogun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An fara wahalar fetur yayin da kudin lita ya karu
Gidajen mai mallakin kamfanin NNPCL kuwa sun cika makil da mutane wanda ya haddasa dogon layi na mutanen da ke son sayan fetur.
Yayin da 'yan bumburutu ke siyar da lita akan naira 1,000, gidajen man MEMAN da suka hada da Eterna, NorthWest, TotalEnergies, Mobil da sauransu na sayar da litar akan naira 615.
An ga yadda motoci da sauran ababen hawa ke dogon layi a gidajen mai da ke bude yayin da fetur din ya fara karanci a jihohin.
NNPCL ya daina ba mambobin IPMAN fetur
Da yawan gidajen mai mallakin 'yan kungiyar IPMAN na a rufe saboda ba su da man, wadanda kuka suka bude suna siyar da lita akan naira 650.
Gidajen mai na IPMAN da ke yankin Ikotun zuwa Jakande ba su bude ba a yau Laraba, wanda ya bar mutane da zabin neman 'yan bumburutu.
Shugaban tashar ajiye kaya ta Satellite, kungiyar IPMAN na Legas ya shaidawa gidan talabijin din cewa NNPCL ta daina sayar masu da fetur a yanzu.
Direbobin dakon mai sun janye daga aikin aiki
Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito a ranar Talata cewa direbobin dakon mai sun janye yajin aikin, tare da ci gaba da dakon fetur.
Wannan ya biyo bayan ganawar da suka yi da karamin ministan albarkatun man fetur, Heineken Lokpobiri, ‘yan kasuwar mai da hukumar kula da man fetur ta Najeriya (NMDPRA).
Asali: Legit.ng