“Ba Mu San Dala Ba Amma Abin da Za Mu Ci Ya Gagare Mu”: Magidanci Ya Yi Maganganu Masu Zafi a Bidiyo
- Wani dattijo ya fito ya koka tare da yin zanga-zanga kan halin da ake ciki na tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayan abinci a Najeriya
- Mutumin ya daura alhakin halin da ake ciki a yanzu kan cire tallafin man fetur, yana mai kira ga Shugaban kasa Bola Tinubu da ya rage farashin man fetur
- Dattijon ya bayyana cewa su basu san dala ba amma abinci da za su a yanzu ya gagare su, ga shi babu aikin da za su yi don samun na siyan abinci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura
Al'ummar Najeriya na ci gaba da kokawa yayin da tsadar rayuwa da hauhawar farashin kaya ke kara kamari a kasar.
Farashin abubuwa, musamman kayan abinci sun yi tashin gauron zabi a kasar sakamakon cire tsallafin man fetur da kuma faduwar darajar naira a kasuwar canji.
Kan haka ne wani dattijo ya fito dandalin soshiyal midiya domin yin zanga-zanga kan halin da ake ciki, ya kuma aika sako ga shugabanni kan halin da talaka ke ciki a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kun kara kudin mai Najeriya ta kasa zama lafiya, dattijo ya koka
A wani bidiyo da ya yadu wanda shafin Mahmud galadanci II ya wallafa a Facebook, an jiyo dattijon yana cewa su basu san dala ba amma abin da za su ci yana neman ya gagere su.
Dattijon ya kuma daura alhakin halin da ake ciki kan cire tallafin man fetur da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi tun bayan da ya karbi ragaramar shugabanci a kasar.
An jiyo mutumin yana cewa:
"Ba rage kudin mai ba mutane suna ta mutuwa, Nawa ake siyar da abinci? Wani aiki za mu yi mu siya abinci? Ace buhun siminti N8,000, N10,000 a gidan wa ake haka?
"Mu mun san dala ne? Ga abin da za mu ci ya dame mu. Haka ake shugabanci? Wani irin shugabanci ne wannan? Ya kamata ku rage mana kudin mai, ku rage kudin mai.
"Duk wannan da ke faruwa a Najeriya kudin mai ne. Kun kara kudin mai Najeriya ta kasa zama lafiya, mutanen Najeriya sun kasa zama lafiya."
Kalli bidiyon a kasa:
Akpabio ya fadi masu daukar nauyin zanga-zanga
A wani labari na daban, mun ji cewa shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio, ya yi iƙirarin cewa wasu ne suka kitsa tare ɗaukar nauyin zanga-zangar da mutane ke yi kan tsadar rayuwa.
Jaridar The Cable ta tattaro cewa mutane sun fito zanga-zanga a sassa daban-daban na ƙasar nan, ta baya-bayan nan ita ce wadda aka yi Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
Asali: Legit.ng