Tsadar Siminti: Gwamnatin Tarayya Ta Jero Yarjeniyoyi 6 da Ta Cimma da Dangote, BUA, Lafarge

Tsadar Siminti: Gwamnatin Tarayya Ta Jero Yarjeniyoyi 6 da Ta Cimma da Dangote, BUA, Lafarge

  • Gwamnatin tarayya ta lissafa wasu yarjejeniyoyi guda shida da ta cimma da kamfanonin siminti bayan ganawar sirri da suka yi a Abuja
  • Ministan ayyuka Sanata Nweze David Umahi ya gana da kamfanonin Dangote, Bua, Lafarge kan tsadar siminti a ƙasar nan
  • A cewar sanarwar da ma'aikatar ayyuka ta fitar, ɓangarorin biyu bayan taron sun amince da sake zama cikin kwanaki 30 don duba irin ci gaban da aka samu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta gana da masu sana’ar siminti kan yadda za a shawo kan tashin farashin siminti a ƙasar nan, inda aka amince da wasu muhimman abubuwa guda shida.

Taron ya samu halartar mai girma ministan ayyuka Sanata Nweze David Umahi GON, ministan masana'antu, ciniki da zuba jari, Dr. Doris Uzoka-Anite, masu samar da siminti (Dangote Cement Plc, BUA Cement Plc, Lafarge Africa Plc) da ƙungiyar masu sana'ar siminti.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Ministan Buhari ya goyi bayan Sarkin Musulmi, ya gaya wa Tinubu abin da zai yi

FG ta gana da masu sarrafa siminti
A ganawar ta su sun cimma yarjeniyoyi shida Hoto: @FMWNig
Asali: Twitter

Waɗanne yarjeniyoyi suka cimma?

A cikin sanarwar da ma’aikatar ayyuka ta fitar a shafinta na yanar gizo, gwamnatin tarayya da masu samar da simintin sun amince da waɗannan abubuwan:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

  • Ƙalubalen da masu sarrafa siminti ke fuskanta

a. Tsadar gas

b. Tsadar harajin shigo da kaya akan kayan gyara

c. Rashin kyawun hanyoyi

d. Tsadar canjin kuɗi

e. Fasa ƙwaurin siminti zuwa ƙasashe makwabta.

  • Gwamnatin tarayya ta lura da ƙalubalen kuma ta amince da ɗaukar matakan da suka dace.
  • Masu sarrafa siminti da gwamnati sun amince cewa tsadar siminti a halin yanzu ba shi da kyau.
  • Don haka, masana'antun siminti sun yarda cewa farashin siminti ba zai wuce tsakanin ₦ 7,000.00 da ₦ 8,000.00/50kg ba ya danganta da wurin.
  • Masu sarrafa siminti sun amince su kafa tsarin sa ido kan farashin don tabbatar da bin ƙa'ida, da hukunta masu sayarwa ko dillalai da aka samu sun saɓa doka.
  • Gwamnatin tarayya ta ce tana sa ran farashin da aka amince da shi zai ragu bayan tabbatar da matakan da gwamnati ta ɗauka kan ƙalubalen da masana'antun ke fuskanta.
  • Ɓangarorin biyu sun amince su sake zama nan da kwanaki 30 don duba irin ci gaban da aka samu.

Kara karanta wannan

Ku bamu kwana 30, Masu sarrafa siminti sun gindaya sharuda ga Tinubu kan farashin, sun kawo mafita

Ma'aikatar ta kuma sanya bidiyon taron a shafinta na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter)@FMWNIG.

Masu Sarrafa Siminti Sun Kawo Mafita

A wani labarin kuma, kun ji cewa masu sarrafa siminti ta Najeriya (CEPAN) ta bayyana cewa a shirye take ta karya farashin siminti cikin kwana 30.

Sai dai ƙungiyar ta buƙaci gwamnatin tarayya ta yi duba zuwa matakan da marigayi tsohon shugaban ƙasa, Musa Yar’adua ya yi a wancan lokacin domin rage tsadar simintin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng