Asiwaju Ana Yunwa: Kabiru Gombe Ya Aikawa Shugaban kasa Muhimmin Sako Wajen Karatu
- Sheikh Kabir Muhammad Haruna Gombe ya yi kira ga gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta duba halin da mafi yawan mutane suka shiga
- Malamin wanda shugaba ne a kungiyar Izala ya ce ana yunwa a kusan ko ina, kyau a bude baitul-mali domin a taimakawa Bayin Allah
- Kabir Gombe bai ga amfanin a tara kudi da nufin yin ayyukan more rayuwa alhali wadanda ake mulka suna neman mutuwa da yunwa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Sheikh Kabir Muhammad Haruna Gombe wanda babban malami ne a Najeriya, ya aika sako zuwa ga Bola Ahmed Tinubu.
Sheikh Kabir Muhammad Haruna Gombe ya yi magana ne duba da irin halin da al’umma su ke ciki, Legit ta samu bidiyon a shafin X.
Da yake bayani, Kabiru Gombe ya ba gwamnati shawarar ta raba abinci domin a samu saukin yunwa da talauci da ya yi katutu a ko ina.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kiran Kabiru Gombe ga Tinubu
"Wallahi, al’umma tana cikin masifa da talauci da yunwa, duk wanda ya fada maka babu wannan, abin bai iso gidansu ba ne."
"Da wannan mu ke kira ga shugaban kasar Najeriya, Alhaji Asiwaju Bola Ahmed Tinubu."
"Mai girma Asiwaju, mutane suna cikin yunwa. Babu lokacin da ya kamata gwamnati ta taimaki kamar irin wannan lokaci."
- Sheikh Kabir Muhammad Haruna Gombe
Tinubu, ina amfanin badi babu rai?
"Mai girma shugaban kasa a bude baitul-malin gwamnati, a debi dukiya a saye abinci, idan akwai abincin a ajiye, a fito da shi.
A sayo abinci a taimakawa talaka. Mun san kuna da burin nan gaba ku yi hanyoyi, idan yunwa ta kashe talaka kafin ranar da za ayi hanyar, menene amfaninta a wajensa?"
- Sheikh Kabir Gombe
Yadda Tinubu zai bar tarihi
Malamin ya ce idan aka raba tireloli na shinkafa, masara, gero, dawa, taliya, sukari da garin tuwo, gwamnatin nan za ta samu albarka.
Sakataren na kungiyar Izala ya kara da cewa za a dauki shekaru masu yawa ana tunawa da Bola Tinubu idan ya saukakawa talaka.
Shehin malamin ya fadawa shugaban kasa akwai sauran kasashen duniya da ba su kai Najeriya yawan arziki ba su ke rayuwa a sauki.
Kabiru Gombe ya ja hankalin gwamnati
Kabiru Gombe bai ga amfanin tara kudi da ake yi bayan cire tallafi ba, domin ya ce za a iya samun irin Godwin Emefiele ya sace dukiyar.
Shahararren malamin ya yi kira ga masu hali da wadata su rika taimakawa marasa shi, ya ce rowa zai jefa kasar a cikin karin bala’i.
An hana abinci barin Najeriya
A lokacin da ake neman abinci a Najeriya, sai aka ji labari an ga manyan motoci dauke da buhunan abinci za su tsallaka kasar Nijar.
Jami’an gwamnati sun bada umarni an maida kayan abincin Najeriya domin saida su a kasuwannin Najeriya domin a samu sauki.
Asali: Legit.ng