Babban Labari: Bayan Kammala Taron AU, Shugaba Tinubu Ya Bar Addis Ababa, Zai Dawo Gida
- Bayan kammala taron kungiyar Tarayyar Afrika karo na 37, shugaban kasa Bola Tinubu ya bar kasar Habasha a safiyar Litinin
- A lokacin da ya ke kasar Habasha, an ruwaito cewa Tinubu ya gana da shugabannin kasashen Afirka kan matsalar tsaro da zaman lafiya
- Hakazalika, ta samu damar halartar taron majalisar zartarwar AU karo na 44 wanda aka tattauna batutuwa da suka shafi ilimi a Afrika
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Adis Ababa, Ethiopia - Shugaba Bola Tinubu ya bar birnin Adis Ababa na kasar Habasha, inda aka gudanar da babban taron kungiyar Tarayyar Afirka karo na 37.
A safiyar yau Litinin da misalin karfe 10 na safe ne shugaban kungiyar ECOWAS ya bar Adis Ababa zuwa Najeriya, Channels TV ta ruwaito.
A lokacin da yake kasar Habasha, shugaban ya halarci zaman taro na 44 na majalisar gudanarwar kasar AU.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma gudanar da tarurruka da wasu shugabannin kasashe, tare da kuma gudanar da wasu ayyukan a gefe guda a taron kungiyar ta AU.
Abubuwan da aka tattauna a ziyarar Tinubu zuwa Habasha
Arise News ta ruwaito shugaba Tinubu ya isa kasar Habasha a ranar Alhamis da karfe 10 na dare, kuma ya samu rakiyar wasu ministoci da wasu manyan jami'an gwamnati.
Tinubu ya bi sahun sauran shugabannin Afirka wajen gudanar da manyan taruka kan sauye-sauyen dokokin tafiyar da kungiyar Tarayyar Afirka; zaman lafiya da tsaro.
An kuma tattauna batutuwan da suka shafi sauyin yanayi, da kuma hanyoyin shiga da tafiyar da kungiyar G20.
Taken taron na shekara shi ne:
"Ilimantar da ɗan Afirka wanda ya dace da karni na 21: Gina tsarin ilimi mai dorewa da bunkasa hanyoyin samun ilimi mai inganci a Afirka."
Asali: Legit.ng