Sabuwar Matsala Ta Ɓullo a Gidajen Man Fetur a Abuja Yayin da NARTO Ta Ɗauki Mataki 1 Rak
- Ƙarancin man fetur ya mamaye babban birnin tarayya Abuja yayin da aka wayi garin Litinin mafi akasarin gidajen mai a rufe
- Wannan na zuwa ne yayin da kungiyar direbobi NARTO ta dakatar da ayyukan manyan tankoki da ke dakon man fetur kan tsadar rayuwa
- Ƴan kasuwa masu zaman kansu ne kaɗai suka buɗe jidajen mai wanda hakan ya haddasa dogon layi da cunkoso
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - An wayi garin ranar Litinin, 19 ga watan Fabrairu, 2024 da dogon layi a gidajen mai da ke birnin tarayya Abuja.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa ƙarancin fetur ya fara mamaye Abuja ne a daidai lokacin da ƙungiyar direbobin manyan motoci (NARTO) ta dakatar da ayyukan tankoki.
NARTO ta bayyana cewa ta dakatar da ayyukann tankokin dakon mai saboda tsadar abubuwa da ke neman cin ƙarfinsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyar ta sanar da Gwamnatin Tarayya da ƙungiyar ƴan kasuwar mai ta Najeriya shirinta na dakatar da ayyukan tanka a faɗin ƙasa.
Yayin da take sa ido kan kasuwancin mai da safiyar Litinin din nan, jaridar The Nation ta lura cewa yawancin gidajen mai sun rufe.
Ƴan ƙasuwar man fetur masu zaman kansu ƙalilan ne suka buɗe gidajen mai kuma an tattaro cewa suna siyar da kowace lita tsakanin N648 zuwa N670.
Baya ga haka kuma akawai ƴan kasuwar bayan fage waɗanda ke siyar da kowace lita ɗaya kan N850 a cikin jarkoki.
Me zai biyo baya sakamakon matakin NARTO?
Da aka tuntuɓe shi ta wayar salula, shugaban ƙungiyar NARTO, Alhaji Yusuf Lawal Othman, ya tabbatarwa ƴan jarida cewa matakin dakatar da ayyukan tankokin mai ya fara aiki.
Ya bayyana cewa wannan matakin da suka ɗauka, zai tsayar da dukkan jigilar man fetur, rahoton jaridar The News.
EFCC ta tsare tsohon gwamnan Kwara
A wani rahoton Jami'an hukumar EFCC sun tasa tsohon gwamnan Kwara, Abdulfatah Ahmed, da tambayoyi kan yadda aka kashe kuɗaɗe a lokacin mulkinsa.
Rahoto ya nuna cewa tsohon gwamnan ya isa ofishin EFCC da ke Ilorin, babban birnin jihar Kwara da safiyar ranar Litinin, 19 ga watan Fabrairu.
Asali: Legit.ng