Kamfanin BUA Zai Yi Wa Ma'aikatansa Abu 1 Bayan Ya Kara Farashin Buhun Siminti
- Abdul Samad Rabiu, shugaban kamfanin BUA, na shirin ƙara albashin ma’aikata a dukkan kamfanoninsa
- Kamfanin ya jaddada sadaukar da kai ga jin dadin ma’aikata, musamman ta la’akari da matsalolin tattalin arzikin da ƙasar nan ke fuskanta a halin yanzu
- Sanarwar ta zo ne bayan manyan kasuwancin kamfanin BUA sun samu ci gaba mai girma a sassa daban-daban
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
A wani muhimmin mataki na ba da fifiko kan jin daɗin ma'aikata, Abdul Samad Rabi'u, shugaban rukunin kamfanonin BUA, ya amince da ƙarin kaso 50% na albashi ga ma'aikatansa.
An bayyana matakin ne ta hanyar wata sanarwa ta cikin gida daga shugaban ma’aikata na rukunin BUA, Mohammed Wali.
Hakan na zuwa ne bayan rahotannin da ke cewa farashin buhun siminti mai nauyin kilogiram 50 ya haura zuwa kusan N9,500 a sassa da dama na birnin Legas da ma sassan ƙasar nan, sakamakon hauhawar da farashin kayayyaki ke yi a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kwanakin baya ne ministan ayyuka David Umahi ya kira masu sana’ar siminti zuwa wani taro a ranar Litinin 19 ga watan Fabrairu domin duba batutuwan da suka shafi tashin farashin siminti.
Dukkan ma'aikata za su amfana
Billionaire.Africa ta ruwaito cewa ƙarin albashin ya nuna yadda rukunin BUA ke kyautata jin dadin ma'aikata kuma ƙarin shafi ma'aikatan dindindin da wadanda ba na dindindin ba.
Ya ƙara da cewa hakan ya nuna yadda Abdul Samad Rabi’u ya jajirce wajen taimaka wa dukkan ma’aikatansa a lokutan wahala da kuma fahimtar matsalolin da suke ciki.
Kamfanin simintin BUA dai yana ɗaya daga cikin na gaba-gaba wajen samar da siminti a Najeriya, inda ya ke samar da ton 11m duk shekara.
Abdulsamad Ya Tafƙa Asara
A wani labarin kuma, kun ji cewa Hamshakin dan kasuwar Najeriya, shugaban rukunin kamfanonin BUA, ya yi asarar dala biliyan 2.7 a cikin dan karamin lokaci.
Abdul Samad Rabiu ya yi asarar wadannan makudan kudaden ne biyo bayan karya darajar Naira da gwamnatin Najeriya ta yi a yunkurin farfado da tattalin arzikin kasar.
Asali: Legit.ng