Shehu Sani Ya Magantu Yayin da Wasu Mata Suka Yi Zanga-Zanga Zigidir Saboda Tsadar Rayuwa
- Tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayan abinci na cigaba da adabar 'yan Najeriya daga bangarori daban-daban
- Wannan hali da ake ciki na tsadar rayuwa a kasar ya sanya wasu dattawan mata yin zanga-zanga zigidir a titi
- Sanata Shehu Sani ya yi martani, inda ya shawarci dattawan da su guji fita titi babu tufafi da sunan zanga-zanga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura
Al'ummar Najeriya na ci gaba da kowawa saboda tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayan abinci da ake fama da su a bangarori daban-daban na kasar.
Lamarin ya kara muni ne tun bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta yi jim kadan bayan ta garbi ragamar shugabanci.
Wannan hali da ake ciki ya sanya wasu mata fitowa yin zanga-zanga zigidir don neman gwamnati ta dauki matakin gaggawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wani bidiyo da ya yadu a dandalin soshiyal midiya, an gano wasu rukunin mata babu kaya suna tattaki saboda wahalhalun da ake sha a kasar.
Shehu Sani ya yi martani yayin da mata suka yi zigidir
Tsohon Sanatan Kaduna, Shehu Sani, ya yi Allah wadai da wannan zanga-zanga da mata suka yi babu kaya a jikinsu.
Sanata Sani ya shawarci dattawan matan da su yi wa kansu fada sanan su guji aikata irin haka a gaba.
A cewar tsohon 'dan majalisar tarayyar, matasan da suka marawa dattawan matan yin wannan zanga-zanga ba za su taba aikata irin haka ba duk fusatar da za su kan halin da ake ciki.
Ya bayyana hakan ne a cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) a ranar Lahadi, 18 ga watan Fabrairu.
Shehu Sani ya rubuta a shafin nasa:
"Na ga bidiyon wasu dattawan mata suna zanga-zanga kan halin da tattalin arziki ke ciki zigidir. Don Allah ku daina zanga-zanga zigidir.
"Matasan mata da mazan da ke goyon bayan irin wannan zanga-zanga basu taba yin zanga-zanga zigidir ba kuma ba su da niyan yin haka, duk kuwa fusatan da za su yi kan matsin rayuwa."
Jigon PDP ya magantu kan tsadar rayuwa
A wani labarin, Dr Segun Showunmi, tsohon ɗan takarar gwamna a jam'iyyar PDP a jihar Ogun, ya tabbatar da cewa nauyin ƙalubalen tattalin arzikin da ƙasar nan ke fuskanta yana kan ƴan Najeriya.
Dr Segun Showunmi, a yanzu yana neman kujerar shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa.
Asali: Legit.ng