Tsadar Rayuwa: Hamshakin Attajiri a Najeriya Yana Yin Kyautar Kudi? Gaskiya Ta Bayyana

Tsadar Rayuwa: Hamshakin Attajiri a Najeriya Yana Yin Kyautar Kudi? Gaskiya Ta Bayyana

  • Wasu rubuce-rubuce a Facebook da sunan Femi Otedola na neman mutane su miƙa bayanan asusunsu don samun tsakanin N100,000 zuwa N250,000, an tantance gaskiyarsu
  • Bincike ya nuna Otedola bai nemi mutane su ba da bayanan asusunsu ba ko kuma ya yi alƙawarin yin tattaunawa ta sirri da kowa
  • Wani rubutu a shafin Facebook na Otedola mai mabiya sama da 17,000, duk da cewa ba a tantance shafin ba, ya gargaɗi mutane kan bayar da bayanansu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

An lura da wasu shafukan Facebook suna yin kyauta, suna yaudarar mutane da sunan hamshakin ɗan kasuwan Najeriya Femi Otedola.

Ɗaya daga cikin shafukan Facebook ɗin ya buƙaci mutane da su bayar da lambobin wayarsu da asusun ajiyarsu na banki a cikin sashin sharhi don karɓan kuɗi tsakanin N100,000 zuwa N250,000.

Kara karanta wannan

Mai tsaron gidan Ivory Coast ya yi amfani da laya a wasan karshe na AFCON 2023

Femi Otedola ba ya rabon kudi
Femi Otedola na daga cikin hamshakan attajirai a Najeriya Hoto: Femi Otedola
Asali: Twitter

Africa Check ta lura cewa shafin Facebook ɗin ya lissafo tarin bankunan Najeriya, inda za a tura kuɗaɗen nan take. Bankunan sun hada da: UBA Bank, Unity Bank, FCMB Bank, Keystone Bank, da Union Bank".

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta kuma bayar da lambar waya guda ɗaya domin mutane su kira "Fasto David Balogun" ga duk mai buƙatar taimako.

Wani shafin Facebook ya buga irin wannan rubutu da sunan Otedola. An kuma yi amfani da hotunansa.

Sai dai kuma babu wata shaida da ke nuna cewa Femi Otedola ne ke gudanar da bada kyautar, wanda hakan ke ƙara nuna fargabar cewa shafukan sada zumunta na Facebook na iya zama damfara.

Otedola yayi gargaɗi game da zamba

Shafin Otedola na Facebook yana da mabiya 17,000. Ko da yake ba a tabbatar da shi ba, hamshakin attajirin ya fito ƙarara ya bayyana cewa shafin shi ne kaɗai yake da shi a Facebook.

Kara karanta wannan

Ba a gama da batun Emefiele ba an bankado wata sabuwar badakala a CBN, bayanai sun fito

Ya kuma gargaɗi mutane da su guji aika kuɗi ga duk wanda ke da’awar alaƙa da shi, ya kuma bayyana cewa ba zai taɓa yin hira da neman kuɗi a wajen kowa ba.

Bambancin da ke tsakanin shafin da ya musanta bayar da kyautar da sauran shafukan da ke yin kyauta shine adadin mabiyan su.

Shafukan bayar kyauta na Facebook suna da mabiya ƴan kaɗan, yayin da shafin Otedola ke da mabiya 17,000.

Otedola ya fito ya musanta bayar da kyautar ne a watan Disamban 2023.

Rubutun ya karanta:

“Ina so in sanar da kowa cewa Femi Otedola ba zai taba yin hira da ku a keɓe ba don neman kuɗi, ko kuma ya ce ku aika wa wani kuɗi. Duk wanda ya aiko da hakan to ba ni bane."

Ƴan Najeriya Sun Kira Ruwa

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jigo a jam'iyyar PDP, ya ɗora alhakin halin matsin da ake ciki a ƙasar nan a kan ƴan Najeriya.

Segun Showunmi ya bayyana cewa ƴan Najeriya suna sane da halin da jam'iyyar APC ta jefa ƙasar nan amma suka sake zaɓenta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng