Yarabawa Sun Goyi Bayan Tinubu, Sun Fadi Mutum 1 da Ya Jefa 'Yan Najeriya Halin da Suke Ciki

Yarabawa Sun Goyi Bayan Tinubu, Sun Fadi Mutum 1 da Ya Jefa 'Yan Najeriya Halin da Suke Ciki

  • Ƙungiyar Yarabawa ta Afenifere ta caccaki masu sukar Shugaba Tinubu kan halin matsin tattalin arziƙi da ake ciki a ƙasar nan
  • Ƙungiyar ta bayyana cewa masu sukar gwamnatin Tinubu sun manta da cewa Buhari ne ya jefa ƙasar nan halin da ake ciki
  • A cewar ƙungiyar masu sukar gwamnatin Tinubun suna jin zafi ne har yanzu saboda nasarar da ya samu a zaɓen 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Ƙungiyar Yarabawa ta Afenifere, ta ce “tabarbarewar tattalin arziki” da ƴan Najeriya ke fuskanta, ya samo asali ne sakamakon rashin ɗaukar matakan da suka dace da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi.

Yayin da ake ƙara nuna damuwa kan tsadar rayuwa tun lokacin da aka kafa gwamnatin Bola Tinubu, Afenifere ta caccaki masu sukar shugaban ƙasar inda ta ce har yanzu suna jin zafin nasarar da ya samu a zaɓen 2023, cewar rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya shiga taron gaggawa da gwamnoni kan muhimman abu 2, bayanai sun fito

Afenifere ta goyi bayan Tinubu
Afenifere ta bukaci a daina ganin laifin Tinubu Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Muhammadu Buhari
Asali: Twitter

Ƙungiyar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da sakataren tsare-tsaren ƙungiyar na ƙasa, Kole Omololu ya fitar ranar Juma'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Waɗanda suke barci da munshari a cikin shekaru takwas na Buhari sun farka kwatsam. Sun manta cewa yakamata a ɗauki waɗannan matakan gyara shekaru da yawa baya.
"Manyan zunubai na Shugaba Tinubu sun ta'allaƙa ne kan jajircewarsa na tsayawa takara da lashe zaɓen shugaban ƙasa."

Shugaba Tinubu dai a farkon fara mulkinsa a watan Mayun 2023, ya kawo ƙarshen tsarin tallafin man fetur tare da mayar da farashin sauya kuɗaɗen waje ya zama ɗaya.

Afenifere ta faɗi laifin Buhari

A cewar Afenifere, waɗannan matakan Buhari ya kau da kai wajen aiwatarwa, inda ta ce ya kamata a yaba wa Shugaba Tinubu, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Ganduje ya fadi lokacin da sauki zai zo kan halin da ake ciki a kasa

Ƙungiyar ta kuma zargi tsohon shugaban ƙasar da rashin gargaɗin tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, wanda ta ce ya buga Naira tiriliyan 22.7 ta tsarin 'Ways and Means'.

Afenifere ta ce wannan katoɓarar ta Emefiele na ɗaya daga cikin dalilan da suka sanya ƙasar nan ta samu kanta a cikin wannan matsalar tattalin arziki.

Shehu Sani Ya Caccaki Sarakunan Arewa

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shehu Sani, ya yi Allah wadai da sukar gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu da sarakunan Arewa ke yi saboda tsadar rayuwa.

Tsohon sanatan na Kaduna ta Tsakiya ya yi mamakin dalilin da ya sa sarakunan suka yi shiru a lokacin Buhari, amma a yanzu suke iya yin magana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng