Rundunar ‘Yan Sanda Ta Kori Jami’ai 3 Saboda Laifi 1 Tak a Jihar PDP
- An kori jami'an 'yan sanda uku daga aiki saboda aikata cin hanci da rashawa da sauran laifukan rashin da'a a jihar Bayelsa
- Kakakin rundunar 'yan sandan ta ce an dauki matakin korar jami'an daga aiki ne saboda fitar da bara gurbin cikinsu
- Shugaban 'yan sandan yankin ne ya tubewa jami'an da aka kora kayan aiki a ranar Laraba, 14 ga watan Fabrairu, a Yenagoa, babban birnin jihar
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Bayelsa - Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen Bayelsa, ta kori wasu jami'ai uku da ke aiki a hedkwatar Zone 16 daga aiki.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, an sallami jami'an tsaron ne saboda aikata cin hanci da rashawa da kuma sauran laifuka na rashin da'a.
An tattaro cewa da farko hukumomin rundunar sun gurfanar da jami'an da aka kora tare da yi musu shari’a kan laifukan da suka shafi “rashin da'a da cin hanci da rashawa."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin wata sanarwa da ta saki a ranar Juma'a, 16 ga watan Fabrairu, a Yenagoa, jami'ar hulda da jama'a na yankin, CSP Ikwo Kelvin Lafieghe, ta ce an dauki matakin ne a kokarin da ake na raba rundunar da bara gurbi.
Lafieghe ta bayyana cewa jami'an da abin ya shafa sune: Sufeto Edet Inamete, Sufeto Jeremiah Oreeke da Sufeto Uche Collins, rahoton Trust Radio.
Wani bangare na sanarwar na cewa:
"A kokarin da ake na raba rundunar 'yan sandan Najeriya da bara gurbi, an tubawa jami'ai uku da ke aiki da daya daga cikin tawagar hedkwatar rundunar, Yenagoa kayansu a ranar 14 ga watan Fabrairu, bayan korarsu daga hukumar 'yan sandan Najeriya.
"Da farko an gurfanar da jami'an da aka kora tare da yi masu shari'a kan dabi’a mara kyau da cin hanci da rashawa.
"An kama su da laifin tuhumar da ake masu, don haka Sufeto Janar na 'yan sanda IGP Kayode Egbetokun, PhD, NPM, ya yanke masu hukuncin kora daga rundunar, wanda ya fara aiki daga 18 ga watan Janairu, 2024.
“Mutanen da abin ya shafa sune , AP/NO: 279374 Sufeto Edet Inamete, AP/NO: 347467 Sufeto Jeremiah Oreeke da AP/NO: 334909 Sufeto Uche Collins."
'Dan sanda ya sharbi kuka a Adamawa
A wani labarin kuma, mun ji cewa wani bidiyo da ya yadu a ranar Laraba, 30 ga watan Agusta, ya nuno lokacin da wani jami'in dan sanda ke sharban kuka wiwi bayan an sallame shi daga aiki saboda ya aikata ba daidai ba.
Rundunar yan sandan jihar Adamawa, ta gurfanar da wasu jami'anta biyu, Inspekta Ahmed Suleiman da PC Mahmood Muhammed wanda ke aiki da hedkwatar rundunar ta Dumne a dakin shari'a.
Asali: Legit.ng