Tsadar Rayuwa: Tsohon Shugaban Kasa Ya Yi Magana, Ya Bayyana Abin da Ya Ke Tsoron Zai Faru
- Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya yi magana kan mawuyacin halin kunci da ‘yan kasar ke ciki na tsadar rayuwa
- Tsohon shugaban kasar ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta dauki matakin gaggawa kan halin da ‘yan Najeriya ke ciki
- Janar din ya bayyana haka ne a yau Juma’a 16 ga watan Faburairu a shafinsa na X kan irin halin kunci da ake ciki
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Neja – Tsohon shugaban Najeriya a mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida ya yi magana kan halin da ake ciki a kasar.
Ibrahim Badamasi ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta dauki matakin gaggawa kan halin da ‘yan Najeriya ke ciki na mawuyacin hali.
"Sun rasa muryarsu karkashin Buhari": Shehu Sani ya magantu yayin da sarakunan Arewa ke sukar Tinubu
Mene tsohon shugaban ke cewa ga Tinubu?
Janar din ya bayyana haka ne a yau Juma’a 16 ga watan Faburairu a shafinsa na X kan irin halin kunci da ake ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon shugaban ya ce ba ya goyon bayan juyin mulki a kasar amma kuma dole Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta taimaki ‘yan kasar.
Ya ce idan har gwamnatin ba ta dauki matakin kawo dauki ga ‘yan kasar ba komai na iya faruwa.
Ya kuma bukaci Shugaba Tinubu ya dauki tsauraran matakai da za su dakile matsalar kafin komai ya rikice a kasar.
A cewarsa:
“Ba na goyon bayan karbar mulki daga hannun farar hula, amma ina rokon Gwamnatin Tarayya ta kawo dauki ga ‘yan Najeriya.
“Idan har ba a dauki matakin gaggawa ba to lamarin zai iya juyawa zuwa wata babbar annoba a kasar.”
Martanin Sultan kan halin kunci
Har ila yau, Sarkin Musulmi ya yi kira makamancin haka inda ya ce abin ya fara fin karfinsu a matsayinsu na sarakunan gargajiya.
Sultan ya ce idan har Gwamnatin Tarayya ba ta dauki mataki ba komai zai iya faruwa don ‘yan kasar sun fusata.
Sarkin ya ce ya na tsoron ranar da matasa za su ki jin maganarsu lokacin da komai ya rikice ba za a iya taro su ba.
Igboho ya yi martani ga Sultan
Kun ji cewa mai fafutukar kafa kasar Yarbawa, Sunday Igboho ya yi martani ga maganar Sarkin Musulmi.
Igboho ya kare gwamnatin Tinubu inda ya ce babu laifinsa saboda bai wuce watanni takawas ba akan mulki.
Asali: Legit.ng