Matashi Ya Rabu da Budurwarsa Saboda Wani Furuci da Ta Yi, ‘Yan Najeriya Sun Yi Martani

Matashi Ya Rabu da Budurwarsa Saboda Wani Furuci da Ta Yi, ‘Yan Najeriya Sun Yi Martani

  • Furucin da wata matashiya ta yi wa saurayinta ya shafi soyayyarsu na shekara daya kuma hakan yasa ya rabu da ita
  • A cewar saurayin nata, tsohuwar budurwar tasa ta ce ba za ta iya yi masa wankin tufafinsa ba idan suka yi aure
  • Matakin da saurayin ya dauka ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya, inda mutane da dama suka jinjina masa kan rabuwa da ya yi da ita

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wata soyayyar shekara daya ta hadu da tangarda saboda furucin da wata budurwa ta yi wa saurayinta.

Wani mai watsa shirye-shirye a shain X @Wizarab10 ne ya wallaa sakon da saurayin ya aike masa ta sirri.

Matashi ya rabu da budurwa saboda kalaman baki
Matashi Ya Rabu da Budurwarsa Saboda Wani Furuci da Ta Yi, ‘Yan Najeriya Sun Yi Martani Hoto: Vladimir Vladimirov
Asali: Getty Images

A cewar sakon da @Wizarab10 ya wallafa shafinsa X, mutumin ya kawo karshen soyayyarsa da matashiyar ne saboda ta ce ba za ta wanke masa tufafinsa idan suka yi aure.

Kara karanta wannan

"Shi ne sila": Budurwa ta caccaki mahaifinta kan ya sake aure watanni 3 bayan mutuwar mahaifiyarta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilinta kuwa shine cewa mahaifiyarta bata yi wa mahaifinta wankin kayansa. Sakon na cewa:

"Na kawo karshen soyayyata na shekara daya saboda ta ce ba za ta iya wankin kayana ba a matsayin mijinta saboda mahaifiyarta bata wanke kayan mahaifinta."

Ga wallafar a kasa:

Kawunan mutane sun rabu kan haka

@DivineAlfred5 ya ce:

"Ta tafi gidan mahaifinta idan bata shirya zaman aure ba.
"Amma kuma, kayan nawa kuma sau nawa? Dukkanku ba za ku iya hada kudi ku siya injin wanki ba?"

@ernextglow ta ce:

"Manya sun yi gaskiya, kafin ka zabi mata, ka zabi mahaifiyarta.
"Za ta yi koyi da mahaifiyarta ne idan ka aure ta, wannan yarinyar tana nuna wa sahibinta dabi'ar mahaifiyarta ne, da gaske haka mahaifiyarta ta yi da mahaiinta, maza ku lura."

@lobzybaby ta ce:

“Kawai dai bata yi amfani da hikima bane. Bata da wayo, kina iya yin hakan ta hanyar da ta dace kuma ku ci gaba da kasancewa tare.”

Kara karanta wannan

Yadda malamin jami'a ya nemi auren daliba a cikin aji a ranar masoya, bidiyon ya yadu

@neishunk ya ce:

"Ka fada mata ba za ka iya daukar dawainiyar iyalin ba saboda mahaifinka bai yi ba."

Matashiya ta sille mahaifinta soso da sabulu

A wani labarin, mun ji cewa wata matashiya 'yar Najeriya ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya yayin da ta zargi mahaifinta da zama silar mutuwar mahaifiyarta.

A wani bidiyon TikTok, @kopona111 ta bayyana cewa ta gwammaci 'kare rayuwarta a kurkuku maimakon yafewa mahaifinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng