“Shi ne Sila”: Budurwa Ta Caccaki Mahaifinta Kan Ya Sake Aure Watanni 3 Bayan Mutuwar Mahaifiyarta

“Shi ne Sila”: Budurwa Ta Caccaki Mahaifinta Kan Ya Sake Aure Watanni 3 Bayan Mutuwar Mahaifiyarta

  • Wata fusatacciyar matashiyar budurwa ta garzaya soshiyal midiya don zargin mahaifinta da hannu a mutuwar mahaifiyarta
  • A cewarta, mahaifinta ya sake aure watanni uku bayan rasuwar mahaifiyarta sannan ya fatattaki kaninta daga gida
  • Matashiyar, wacce har yanzu take alhinin mutuwar mahaifiyarta, ta bayyana cewa ta gwammaci tafiya kurkuku da ace ta yafewa mahaifin nata

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wata matashiya 'yar Najeriya ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya yayin da ta zargi mahaifinta da zama silar mutuwar mahaifiyarta.

A wani bidiyon TikTok, @kopona111 ta bayyana cewa ta gwammaci 'kare rayuwarta a kurkuku maimakon yafewa mahaifinta.

Budurwa ta koka saboda mahaifinta ya sake aure bayan mutuwar mahaifiyarta
“Shi ne Sila”: Budurwa Ta Caccaki Mahaifinta Kan Ya Sake Aure Watanni 3 Bayan Mutuwar Mahaifiyarta Hoto: @kopona111
Asali: TikTok

@kopona111 ta saki hotunan mahaifinta yayin da ta bayyana cewa ya sake aure watanni uku bayan mutuwar mahaifiyarta.

Kara karanta wannan

Yadda malamin jami'a ya nemi auren daliba a cikin aji a ranar masoya, bidiyon ya yadu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta kara da cewar ya fatattaki kaninta daga gidan mahaifiyarsu sannan ya tare da sabuwar matarsa. @kopona111 ta rubuta:

"Mahaifiyata ita ce sarauniyata kuma lokacin da ta mutu mahaifina ya sake aure cikin watanni 3 sannan ya kori kanina daga gidan mahaifiyata sannan ya tare da sabuwar matarsa kuma duk shi ne silar mutuwar mahaifiyata."

Jama'a sun yi martani

that very PH Girl ta ce:

"Mahaifinki da mahaifina tagwaye ne, ba zan taba yafe masa koda a cikin kabarinsa, wannan mutumin ya nuna mana mugunta ni da 'yan uwana."

Lucius ta ce:

"Ban samu soyayyar uwa ko na uba ba...bana ganin kimar tsoffin mutane kuma...suna amfani da tsufarsu wajen razana matasa."

ezeigbokelechi ta ce:

"Labari iri guda muke da shi amma Allah zai yi mana yaki."

fyrretuioooyy ta ce:

"Allah ya kwashewa mutumin, ba zai ga gobe ba ku tayani cewa amin."

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Amarya ta hallaka mijinta a jihar Neja

BECKY TV ta ce:

"Mahaifiyarku ce ta haddasa komai, menene dalilin da yasa bata sanya sunanta kan takardunta ba."

Malami ya nemi auren dalibarsa a aji

A wani labarin, mun ji cewa Anucha Wisdom, wani malami a jami'ar jihar Abia (ABSU), ya nemi auren wata daliba a cikin aji a ranar masoya.

Malamin ya tsuma zuciyar matashiyar yayin da ya durkusa a gabanta dauke da zobe a hannunsa inda sauran dalibai suk dungi karfafa mata gwiwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng