Ana Fama da Yunwa a Najeriya, Tinubu Ya Yi Sabbin Nada-Nade a Manyan Hukumomi 2, Bayanai Sun Fito

Ana Fama da Yunwa a Najeriya, Tinubu Ya Yi Sabbin Nada-Nade a Manyan Hukumomi 2, Bayanai Sun Fito

  • Shugaban kasa, Bola Tinubu ya amince da nadin wasu manyan shugabanni a hukumomin biyu a Najeriya
  • Tinubu ya amince da nadin shugabannin hukumomin NAFDAC da kuma NCDC a yau Alhamis 15 ga wata Faburairu
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da haidmin shugaban a bangaren yada labarai Ajuri Ngelale ya fitar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Yayin da ake cikin wani hali a Najeriya, Shugaba Tinubu ya yi sabbin nade-nade a manyan hukumomin kasar.

Tinubu ya amince da nadin shugabannin hukumomin NAFDAC da kuma NCDC a yau Alhamis 15 ga wata Faburairu.

Tinubu ya yi sabbin nade-nade a manyan hukumomi 2
Tinubu Ya Yi Sabbin Nada-Nade a Manyan Hukumomi 2. Hoto: Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Yaushe Tinubu ya yi sabbin nade-naden?

Shugaban ya amince da nadin Mansur Kabir a matsayin shugaban kwamitin hukumar kula da magani da abinci ta NAFDAC.

Kara karanta wannan

NMDGIFB: Majalisar Dattawa ta tabbatar da wani muhimmin nadin shugaba Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, Tinubu ya sake nada Mojisola Adeyeye a matsayin babban daraktan hukumar ta NAFDAC.

Sai kuma amincewa da nadin Oladije Idris a matsayin babban daraktan hukumar dakile yaduwar cututtuka ta NCDC.

Wannan nadin na zuwa ne yayin da 'yan kasar ke cikin wani irin hali na tsadar rayuwa tun bayan cire tallafin mai da kuma kokarin cire na bangaren wutar lantarki.

Tinubu ya amince da 'yan sandan jihohi

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin shugaban a bangaren yada labarai Ajuri Ngelale ya fitar.

Har ila yau, Shugaba Tinubu ya amince da kirkirar 'yan sandan jihohin don dakile matsalar tsaro.

Ganawar ta kuma shafi halin da 'yan kasa ke ciki musamman na tsadar rayuwa da kuma neman mafita kan matsalar.

Wannan na zuwa ne bayan ganawa da shugaban ya yi da gwamnonin jihohin yau Alhamis 15 ga watan Faburairu a Abuja.

Kara karanta wannan

Yayin da ya fara hucewa kan rashin nasarar Super Eagles, Tinubu zai shilla wata kasa, an fadi dalili

An bukaci Tinubu ya saka tallafi a aikin hajji

A baya, kun ji cewa Majalisar Dokokin Najeriya ta bukaci gwamnatin Tarayya ta saka tallafi a bangaren aikin hajji.

Majalisar ta tura bukatar ce don rage tsadar kujerar da kuma bai wa mutane damar iya biyan kudaden cikin rahusa.

Wannan na zuwa ne yayin da ake kokawa kan tsadar kujerar a kasar wanda aka saka har naira miliyan 4.9.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.