Shugaba Tinubu Ya Shiga Taron Gaggawa da Gwamnoni Kan Muhimman Abu 2, Bayanai Sun Fito

Shugaba Tinubu Ya Shiga Taron Gaggawa da Gwamnoni Kan Muhimman Abu 2, Bayanai Sun Fito

  • Bola Ahmed Tinubu da gwamnonin jihohi 36 sun shiga taron gaggawa kan tsadar rayuwa da matsalar tsaro da ke ƙara taɓarɓarewa a ƙasar nan
  • Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima da IG na rundunar ƴan sanda na cikin waɗanda aka gani sun shiga wannan taro a Aso Villa
  • Wannan na zuwa ne bayan shugaban ƙasa ya ɗauki wasu matakai da nufin shawo kan tsadar kayan abinci da sauran ƙalubalen tattalin arziki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya shiga taron gaggawa da gwamnonin jihohin Najeriya a ɗakin taron fadar shugaban ƙasa da ke birnin tarayya Abuja.

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ministan Abuja, Nyesom Wike, da Sufetan ƴan sanda na ƙasa, Kayode Egbetokun, sun halarci wannan taro yau Alhamis.

Kara karanta wannan

Jerin gwamnonin da suka halarci ganawa da Shugaba Tinubu kan tsadar abinci da muhimmin abu 1

Shugaba Tinubu na ganawar gaggawa da gwamnoni a Villa.
Shugaba Tinubu da gwamnoni sun shiga taron gaggawa a Villa kan muhimman abu 2 Hoto: Ajuri Ngelale
Asali: Twitter

Kamar yadda The Nation ta ruwaito, an fara taron da misalin ƙarfe 11:30 na safiyar ranar Alhamis, 15 ga watan Fabrairu, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tattaro cewa shugaba Tinubu ya kira taron ne da nufin lalubo hanyoyin magance tsadar kayan abinci, rashin tsaro da sauran batutuwan da suka shafi tattalin arziki.

Wane matakai Tinubu ya ɗauka na rage wa mutane wahala?

Tuni dai shugaban ƙasar ya umurci tawagarsa ta fannin tattalin arziki da suka hada da dukkan jami’an gwamnati da su nemo hanyar da za a gyara lamarin.

Bayan haka Tinubu ya umarci kwamitinsa na ɓangaren agajin gaggawa da ya fito da tan 102,000 na kayan abinci da suka haɗa da shinkafa, masara da gero domin a rabawa talakawa.

Bayanai sun nuna cewa taron gaggawa da ake yi yanzu haka zai lalubo mafita kan yadda za a rage tsadar kayan abinci, da rashin tsaro, Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu zai gana da gwamnonin Najeriya kan muhimmin abu, bayanai sun fito

Gwamnonin da suka halarci taron

Gwamnonin da aka hango sun shiga ɗakin taron a fadar shugaban ƙasa sun haɗa da na jihohin Ekiti, Delta, Borno, Legas, Kwara, Nasarawa da Edo.

Haka kuma an ga gwamnonin Yobe, Anambra, Akwa Ibom, Abiya, Filato, Kaduna, Sakkwato, Neja, Taraba, Adamawa, Kuros Riba, Ogun da Enugu, sun halarci zaman.

Bayan taron gaggawar, za a gudanar da taron majalisar tattalin arzikin kasa na wata-wata wanda mataimakin shugaban kasa, Shettima zai jagoranta.

Tinubu ya aike da saƙo ga majalisar dattawa

A wani rahoton na daban Bola Ahmed Tinubu ya yi sabon naɗi yayin da ƴan Najeriya ke kuka kan taadar rayuwa da wahalar da aka shiga a faɗin kasar

Shugaban ƙasar ya nemi majalisar dattawa ta tantance tare da tabbatar da naɗin Dakta Kelechi Ohiri a matsayin darakta janar na hukumar NHIA

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262