Dakarun EFCC Sun Kai Samame Ɗakunan Ɗaliban Fitacciyar Jami'ar Tarayya Cikin Dare, Bayanai Sun Fito

Dakarun EFCC Sun Kai Samame Ɗakunan Ɗaliban Fitacciyar Jami'ar Tarayya Cikin Dare, Bayanai Sun Fito

  • Jami'an hukumar EFCC sun kai samame ɗakunan kwanan ɗaliban jami'ar fasaha ta tarayya (FUTA) da ke Akure, babban birnin jihar Ondo
  • Bidiyoyin da ke yawo a kafafen sada zumunta sun nuna yadda jami'an suka kutsa cikin ɗakunan ta tsiya, an ce sun kama ɗalibai masu yawa
  • A baya dai shugaban EFCC na ƙasa ya bada umarnin dakatar da kai samame cikin dare bayan abinda ya faru a jihar Osun

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Katsina - Wasu jami'ai da ake kyautata zaton dakarun hukumar yaƙi da rashawa (EFCC) ne sun kai samame jami'ar fasaha ta tarayya da ke Akure (FUTA) a jihar Ondo.

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, jami'an sun kai samame ɗakin kwanan ɗaliban makarantar da tsakar dare misalin ƙarfe 2:00.

Kara karanta wannan

"Ba zamu yarda ba" Sabuwar zanga-zanga ta ɓarke a jihar Arewa, harkoki sun tsaya cak kan abu 1

Jami'an EFCC sun kai samamen cikin dare jami'ar FUTA.
Jami'an EFCC Sun Kai Samame Jami'ar FUTA, Sun Kama Dalibai da Dama Hoto: FUTA, EFCC
Asali: Facebook

Wasu daga cikin ɗaliban jami'ar sun garzaya kafafen sada zumunta, inda suka wallafa bidiyoyin yadda mutanen suka kutsa ɗakuna, suka cafke abokan karatunsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A faya-fayan bidiyoyin da ke yawo a soshiyal midiya, an ga fasassun tagogi wanda ke nuna an shiga ciki da tsiya.

Wani mai amfani da kafar sada zumunta mai suna J Brandy ya rubuta cewa:

"Na ɗauka sun ce EFCC ba zata sake kai farmaki cikin dare ba. Wannan masauki (Celebrity Lodge, FUTA) yana bayan namu. Yaushe za a daina wannan abun? Jami'an EFCC na zuwa wuri kamar barayi da dare."

An ga wani mutum sanye da rigar EFFC a daya daga cikin faifan bidiyo da ke yawo a yanar gizo, kamar yadda Sahara Reporters ta rahoto.

EFCC ta daina kai samame cikin dare

A watan Nuwamba, 2023, Shugaban Hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ya bayar da umarnin a dakatar da samamen aiki cikin dare.

Kara karanta wannan

Labari mai daɗi: Ƴan kasuwa sun rage farashin kayan masarufi, talakawa zasu samu sauƙin sayen abinci

Ya bada umarnin ne bayan kamen da jami'an EFCC suka yi na ƴan damfarar yanar gizo a Ile-Ife, jihar Osun wanda ya tada hazo a faɗin Najeriya.

Da aka tuntubi mai magana yawun hukumar EFCC, Dele Oyewale kan lamarin a ranar Laraba, ya bukaci wakilin jaridar da ya sake kira nan da mintuna 20.

Sai dai har kawo yanzu da muke haɗa muku wannan rahoton bai sake ɗaga kiran wayar da aka masa ba.

Tinubu ya aike da sako ga majalisar dattawa

A wani rahoton na daban Bola Ahmed Tinubu ya aike da sako ga majalisar dattawan Najeriya kan naɗin shugaban hukumar jin daɗin alhazai da mambobi

Shugaban ƙasar ya buƙaci sanatocin su tantance tare da amincewa da mutanen da ya naɗa bisa la'akari da kundin dokar NAHCON.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262