Shugaba Tinubu Ya Aike da Buƙata 1 Ga Majalisar Dattawa Kan Mutanen da Ya Naɗa a NAHCON
- Bola Ahmed Tinubu ya aike da sako ga majalisar dattawan Najeriya kan naɗin shugaban hukumar jin daɗin alhazai da mambobi
- Shugaban ƙasar ya buƙaci sanatocin su tantance tare da amincewa da mutanen da ya naɗa bisa la'akari da kundin dokar NAHCON
- Sanata Akpabio ya miƙa takardar ga kwamitin harkokin waje domin gudanar da aiki na gaba kana ya kawo rahoto a kwanaki 10
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci majalisar dattawan Najeriya ta tantance tare da tabbatar da mutanen da ya naɗa a hukumar jin daɗin alhazai ta ƙasa (NAHCON).
Tinubu ya buƙaci majalisar dattawan ta amince da naɗin shugaban NAHCON da sauran waɗanda ya naɗa a matsayin mambobin majalisar gudanarwa na hukumar.
Hakan na ƙunshe ne a wata wasika da shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio, ya karanta a zauren majalisa ranar Talata, 13 ga watan Fabrairu, The Nation ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasiƙar shugaban ƙasa Tinubu ta ce:
"Bisa tanadin kundin dokokin hukumar jin daɗin alhazai ta ƙasa 2006, ina mai gabatar da sunayen shugaba da mambobin majalisar gudanarwan NAHCON ga majalisa domin tantance su da tabbatarwa.
"Jalal Arabi a matsayin shugaban hukumar, Aliyu Abdulrazaq a matsayin kwamishinan tsare-tsare da kuɗi, Anofi Elegushi a kwamishinan ayyuka da Abubakar Yagawal a kwamishinan tsare-tsare da bincike.
"Ina fatan wannan buƙata tawa zata samu karɓu a majalisar dattawa."
Majalisa ta gano kuskuren Tinubu a NAHCON
Da yake jawabi bayan kammala karanta wasiƙar, Sanata Akpabio ya ce ya duba wasu sassa a kundin dokokin hukumar jin daɗin alhazai NAHCON.
Ya ce ya gano cewa dokar ta tanadi mambobin majalisar gudanarwan NAHCON su fito daga shiyyoyi shida da muke da su a ƙasar nan, Premium Times ta ruwaito.
Akpabio ya ce zasu tuntubi ofishin shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa domin majalisar dattawa na tsammanin ganin sunayen mambobi daga shiyyoyi 6.
Daga nan sai ya mika takardar ga kwamitin kula da harkokin ƙasashen waje domin ɗaukar matakai na gaba kuma ya kawo rahoto cikin kwanaki 10.
Tinubu ya naɗa daractocin CBN 5
A wani rahoton na daban Bola Ahmed Tinubu ya aike da sunayen mutum 5 da ya naɗa a matsayin daraktoci a babban bankin Najeriya (CBN) ga majalisar dattawa.
Sanata Godswill Akpabio, ya karanta sunayen mutanen ga sauran sanatoci a zaman majalisar na ranar Talata a Abuja.
Asali: Legit.ng