Tinubu Ya Gana da Shugabannin Kwadago Yayin da Suke Shirin Shiga Yajin Aiki, Bayanai Sun Fito

Tinubu Ya Gana da Shugabannin Kwadago Yayin da Suke Shirin Shiga Yajin Aiki, Bayanai Sun Fito

  • Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Bola Tinubu da ƙungiyoyin ƙwadago sun gana a Abuja kan wa'adin yajin aikin makonni biyu da NLC da TUC suka bayar
  • Tawagar gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin ƙaramar ministar ƙwadago da samar da ayyuka, Nkeiruka Onyejeocha, ta yi alƙawarin cewa za a gaggauta biyan albashin ma’aikata daga yanzu, inda ta buƙaci ƙungiyar ta dakatar da wa’adin
  • Sai dai NLC da TUC ba su sauka daga kan bakansu ba, inda suka nemi gwamnatin Tinubu ta cika yarjejeniyar da suka cimma a watan Oktoba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Bola Tinubu ta gana da shugabannin ƙungiyoyin kwadagon Najeriya NLC da TUC kan wa’adin kwanaki 14 na yajin aiki da suka bayar.

Kara karanta wannan

Zanga-zanga ta barke a Abuja, hotuna da bidiyo sun bayyana

Ƙaramar ministar ƙwadago da samar da aikin yi, Nkeiruka Onyejeocha, ta wakilci shugaban ƙasar, wanda ya yi alƙawarin cewa biyan albashin ma’aikata zai kasance ba tare da ɓata lokaci ba daga yanzu.

FG ta gana da kungiyoyin kwadago
Gwamnatin Tinubu ta gana da kungiyoyin kwadago na NLC da TUC Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Nigeria Labour Congress
Asali: Twitter

NLC, TUC sun sanar da shirin yajin aiki

Idan ba a manta ba a makon da ya gabata ne ƙungiyoyin NLC da TUC suka bayyana cewa za su fara yajin aiki a fadin ƙasar nan saboda halin ƙuncin da ake ciki a ƙasar nan, sakamakon cire tallafin man fetur da kuma faɗuwar darajar Naira.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙungiyoyin ƙwadagon sun yi zargin cewa gwamnatin Tinubu ta gaza aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma a ranar 2, ga watan Oktoban 2023.

Amma a ranar Talata, 13 ga watan Fabrairu, rahotanni sun ce shugabannin ƙwadagon, sun gana da ministar, inda aka ba su tabbacin cewa gwamnati na ƙoƙarin ganin an aiwatar da yarjejeniyar cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Sarkin Musulmi ya samo mafita ga 'yan Najeriya

Tinubu yayi alƙawarin mutunta yarjejeniya da ƙungiyoyin ƙwadago

A wani saƙo da NTA ta wallafa a shafinta na Twitter, Onyejeocha ta buƙaci ƙungiyoyin NLC da TUC da su janye wa’adin, amma ƙungiyoyin sun tsaya tsayin daka inda suka buƙaci gwamnati ta cika alƙawuran da ta ɗauka.

A taron da suka yi a watan Oktoba, gwamnati da shugabannin ƙwadago sun cimma matsaya guda 16.

Wani ɓangare na rubutun NTA na cewa:

"Onyejeocha ta kuma yi kira ga ƙungiyoyin ƙwadagon da su janye wa’adin kwanaki 14 na yajin aikin, saboda gwamnati ta ƙara kaimi wajen ganin an kammala aiwatar da yarjejeniyar.”

Mahalarta taron sun haɗa da shugaban NLC, Joe Ajaero, da mataimakin shugaban TUC, Tommy Okon.

NLC Ta Magantu Kan Gwamnoni

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC), Joe Ajaero, ya ce galibin gwamnonin da aka sa a kwamitin mafi larancin albashi mai mambobi 37 ba su iya biyan ma'aikatan jihohinsu.

Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Ƙashim Shettima, ya rantsar da kwamitin wanda zai sake nazari kan mafi ƙarancin albashin ma'aikata a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng