Fitaccen Malami Ya Yi Hasashen Sabon Farashin Naira Kan Dala, Ya Ce Buhun Shinkafa Zai Kai 90k
- Primate Elijah Ayodele ya yi sabon hasashen mai daga hankali yayin da darajar naira ke ci gaba da faduwa kan dalar Amurka
- Malamin addinin ya bayyana cewa farashin buhun shinkafa zai koma N90,000 a gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu
- Primate Ayodele ya kuma bayyana sabon farashin chanji yayin da farashin kaya ke ci gaba da hauhawa da kuma tsadar rayuwa
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Yayin da ake tsaka da fama da matsin rayuwa sakamakon manufofin tattalin arziki na gwamnatin tarayya, Primate Elijah Ayodele, na cocin INRI, ya yi gagarumin gargadi ga Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Malamin addinin ya bayyana cewa Najeriya za ta fuskanci durkushewar tattalin arziki idan ba a dauki matakan gaggawa ba, rahoton Daily Post.
Ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mai taimaka masa kan harkokin labarai, Osho Oluwatosin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Primate Ayodele ya bayyana cewa idan Shugaban kasa Tinubu bai yi abin da ya kamata ba, tattalin arzikin Najeriya ba zai daidaita ba har sai a 2026, rahoton Nigerian Tribune.
Farashin shinkafa zai kai N90,000, Ayodele
Babban faston ya yi hasashen cewa dala za ta kai N1,700 sannan buhun shinkafa zai haura N90,000 idan har ba a aiwatar da wani kwakkwaran mataki na magance rudani da al'ummar kasar ke ciki a halin yanzu ba.
A cewar Ayodele:
“Akwai bukatar su samar da tsaro, rage farashin kayayyakin abinci, samar da isasshiyar wutar lantarki da inganta kayayyakin cikin gida. Wannan zai taimaka wa gwamnati kuma zai karya darajar dala.
‘’Duk wadannan matakan da suke dauka ba za su yi tasiri ba; kawai dai zai haifar da hauhawar farashin kayayyaki ne.
"Idan ba su yi abin da ya dace ba, Najeriya za ta sayi dala kan N1,700, buhun shinkafa zai kai N90,000 sannan zai kashe tattalin arzikin kasar.
"Da alama ba su da masaniya cewa hakan ba zai taimakawa halin da ake ciki ba.''
An bukaci Tinubu ya kawo karshen yunwa
A wani labarin, mun ji cewa mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya ƙarbi baƙuncin uwargidan shugaban ƙasa, Remi Tinubu a fadarsa da ke birnin Kano.
Sarkin na Kano a yayin ziyarar da uwargidan Tinubu ta kai masa, ya miƙa mata saƙonni waɗanda za ta ba shugaban ƙasan idan ta koma, cewar rahoton Daily Trust.
Asali: Legit.ng