Kungiyar Kare Muradin Arewa Ta Tsawatar Kan Tsadar Rayuwa Da Tsaro a Yankin

Kungiyar Kare Muradin Arewa Ta Tsawatar Kan Tsadar Rayuwa Da Tsaro a Yankin

  • Dattawan Arewa karkashin kungiyar 'Arewa New Agenda' (ANA) ta zauna ta fitar da shawarwari da za ta bai wa gwamnatin tarayya don magance kallubalen rashin tsaro da talauci a yankin
  • Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Yayale Ahmed, ya ce za su tattauna da gwamnatin tarayya su gabatar mata da shawarwarin tare da tsare-tsaren da ake fatan za su warware matsalolin da ke adabar yankin
  • Sanata Ahmad MohAllahyidi, jagoran ANA ya lissafa tsare-tsaren da dattawan arewan suka fitar da suka hada da tallafawa masu karamin karfi su 100,000 a jihohi 19 na arewa, bullo da hanyoyin inganta aikin noma da makamashi na zamani da sauransu

Abuja - Manyan 'yan Arewa, karkashin kungiyar Arewa New Agenda (ANA), za su tunkari gwamnatin tarayya da wasu shawarwari kan yadda za a magance kallubalen tsaro da tsayar rayuwa a yankin.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Gwamnonin PDP sun nemi Tinubu ya yi murabus, sun fadi dalili

A cewar dattawan, shawarwarin idan an aiwatar, za su kawo cigaba mai dorewa a arewa da ma kasa baki daya.

Dattawan arewa sun bai wa FG shawarwarin magance matsalar tsaro da talauci
Dattawan arewa sun bai wa gwamnatin tarayya shawarwarin warware matsalar tsaro da talauci a yankin
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayale Ahmed, tsohon sakataren gwamnatin tarayya (SGF) ya bayyana cewa dattawan za su tattauna da gwamnatin tarayya don gabatar da tsare-tsaren da nufin warware matsalar fatara da talauci a arewa.

A wurin taron, akwai tsaffin gwamnoni: Isa Yuguda da Sani Yerima; Sanata Jonathan Zwingina, Hon. Babangida Ngoruje, tsohon shugaban ma'aikatan tarayya; Danladi Kifasi; Ambasada Fatima Adams; da Ciyaman din Hukumar Hajji ta Kasa, Jala Arabi da wasu da dama.

Ahmed ya ce, a matsayinmu na dattawa:

"Mun amince mu yi wa Najeriya hidima da daukaka Arewa, ba don mun cire tsammani ba amma domin mu masu tunkarar gaskiya ne.
"Mun son canja salo da tsare-tsaren magance batutuwa da matsalolin arewacin Najeriya.
"Nauyin da ya rataya a kanmu ba wai mu ce gwamnati ta gaza ba, gwamnati za ta yi aiki ne da gudunmawarmu, gwamnati za ta yi abin da ya dace idan mun yi, gwamnati za ta jajirce idan mun jajirce.

Kara karanta wannan

Murna yayin da gwamnan APC ya fara raba kayan tallafi na biliyan 5 ga mabukata

"Mu 'yan Najeriya ne masu kishin kasa, za mu sanar da wadanda ke rike da madafan iko abin da muka yanke don inganta rayuwar mutane baki daya."

Dattawan arewa sun bada shawaran warware matsalar yankin
Kungiyar ANA za ta gabatarwa gwamnatin tarayya shawarwarin magance matsalar talauci da tsaro.
Asali: UGC

Jagoran ANA, Sanata Ahmad MohAllahyidi, yayin da ya ke gabatar da shawarwarin, ya yi bayanin cewa sakamakon tattaunawa da aka yi ne na taron ANA na kwana guda a Nuwamban 2023 inda aka tattauna kan matsalan yawan laifukan da matasa ke yi a arewa, laifuka da ke damun yankin da ke cigaba da zurfafa talauci a yankin da hanyar da za a magance.

Bayan hakan, ya ce dattawan sun fitar da shawarwari da tsare-tsare, ciki da hanyar kawo cigaba da suka hada da koyar da sana'a ga mutane masu rauni, rahoton The Nation.

Wane shawarwari ANA ta bai wa gwamnatin tarayya don ceto arewa?

Ya ce matakin na farko zai tallafawa mutane masu rauni 100,000 a duk jiha don inganta ayyuka cikin watanni 15.

Kara karanta wannan

"Ya dauki nauyin kawunnai na 10 zuwa Hajji": Tambuwal ya tuna haduwarsu ta karshe da Wigwe

Shawara na biyu ya shafi noma, duba da cewa galibin arewacin Najeriya kamar sauran kasar, sun dogara ne sosai kan noma don tattalin arzikinsu.

A cewar MohAllahyidi, duk da kasar noma a Najeriya, kashi 35% na kasar noman ne kacal ake amfani da shi, ANA na goyon bayan shirin gwamnatin tarayya na fadada noma zuwa kashi 65% a cikin shekara hudu.

Kungiyar ta kuma bada shawarar kafa cibiyoyi na Inganta Ayyuka a kowanne jiha 19 na arewa.

Wannan shirin zai samar da ayyuka kimanin miliyan 10 ga matasa da sauran al'umma.

MohAllahyidi ya ce:

"Wannan tsarin zai iya samar da fiye da tiriliyan 50 duk shekara, yayin da ta'addanci, fashi da makami da sauran munanan ayyuka za su ragu sosai.
"Shirin zai kuma inganta kudaden shiga daga kasashen waje tare da daidaita tattalin arzikin mu.
"Koyar da matasa fasahar makamashi marasa karewa (hasken rana (solar) iska, da Biomass) a matsayin sana'a zai inganta yaki da sauyin yanayi.

Kara karanta wannan

Sabuwar baraka ta kunno kai yayin da tsohuwar hadimar Buhari ta caccaki Tinubu, an yi karin bayani

"Wannan tsarin taimako ne ga al'umma kuma ana sa ran zai kawo sauyi da gidaje fiye da 1000 a duk jiha a jihohi 19.
"Wani shawarar shine amfani da fasahar noman zamani na 'Tissue culture' don rubanya iri. Wannan tsarin zai iya samar da iri miliyan biyu duk shekara."

Bugu da kari, ANA ta jadada bukatar da ke akwai na gwamnatin tarayya ta taimakawa jihohin arewa ta hanyar amfani da dokar Kafa Sabbin Sana'o'i ta 2022, wanda zai bai wa kamfanoni a yankin daman yin binciken zamani, bada horaswa da samar da kayayyakin da duniya za ta iya amfani da su.

Bayan nusantar da cewa yana da muhimmanci a bukaci kwamitin da ke nazarin shirin ya kasance mai himma wajen cika aikinsa, MoAllahyidi ya ce:

"Yana da muhimmanci a bukaci kwamitin da ke nazarin shirin ya zurfafa nazari kan tasirin shirin da amfaninsa don ganin ya kai ga masu rauni da ke bukatarsa sosai.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibai masu ɗimbin yawa a jihar Arewa, gwamna ya magantu

"Hakan zai bai wa shirin damar cimma manufarsa a yayin da tattalin arzikin kasar ke kara tabarbarewa.
"Dakatar da shirin ya kamata ya bada daman sauya kallon da al'umma ke yi wa rashin tabuka aiki da NSIP ta yi ta hanyar koyan darasi daga kasashen duniya kamar Cuba, Bangladesh, Tanzania da suka yi nasarar kai wa ga al'umma a masa garambawul ya dace da mu."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164