Jami'an Hukumar NDLEA Sun Cafke Mai Safarar Miyagun Kwayoyi Ga 'Yan Ta'adda, Bayanai Sun Fito
- Jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) sun caffke masu safarar miyagun ƙwayoyi a sassa daban-daban na ƙasar nan
- Daga cikin waɗanda ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyin ciki har da mai safararsu ga ƴan ta'adda a jihar
- Daraktan yaɗa labarai na hukumar wanda ya tabbatar da kamen ya ce an cafke mai safarar ƙwayoyin ga ƴan ta'adda ne a yankin Banki na jihar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) ta sanar da cafke wani mai safarar ƙwayoyi ga ƴan ta'adda a jihar Borno.
Hukumar ta ce ta cafke Ahmad Mohammed ɗan shekara 42 da haihuwa da laifin safarar ƙwayoyi ga ƴan ta'adda da ke ɓoye a yankin Banki da ke jihar Borno.
Hukumar ta ce wanda ake zargin yana ɗaya daga cikin mutum 24 da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi da dillancinsu, waɗanda aka kama a wasu hare-hare daban-daban a jihohi takwas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NDLEA ta cafke masu safarar miyagun ƙwayoyi
Daraktan yaɗa labarai na hukumar NDLEA da ke Abuja, Femi Babafemi, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, 11 ga watan Fabrairu a birnin tarayya Abuja.
Babafemi ya kuma ce waɗanda ake zargin sun haɗa da wata mace mai cikin wata shida, wata mata mai ƴaƴa uku da wasu mata uku.
Babafemi ya ce jami’an hukumar sun kama sama da kilogiram 7,609 na haramtattun ƙwayoyi.
Sanarwar ta ci gaba da cewa:
"A jihar Borno, jami'an NDLEA sun kama wani mutum mai suna Ahmad Mohammed mai shekara 42, da ake zargi da kai wa ƴan ta’adda miyagun ƙwayoyi a Banki, da ke kan iyaka tsakanin Najeriya da Kamaru.
"Jami’an NDLEA sun kama Ahmad Mohammed ne a ranar Juma’a 9 ga watan Fabrairu a shingen bincike na Bama.
"A lokacin da aka bincike jakunkunansa an gano ƙwayoyin tramadol guda 20,000 daga hannunsa a lokacin da yake kan hanyarsa ta kai kayan a garin wanda yake a kan iyaka."
NDLEA Na Neman Sarauniyar Kyau
A wani wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA), na neman wata tsohuwar sarauniyar kyau bisa zargin safarar miyagun ƙwayoyi.
Matar wacce aka fi sani da Ms. Queen Oluwadamilola Aderinoye, ita ce sarauniyar kyau ta Commonnwealth Nigeria Culture a shekarun 2015/2016.
Asali: Legit.ng