Zanga-Zanga Kan Tsadar Rayuwa Ta Ci Gaba da Yaduwa a Sassan Najeriya, Bayanai Sun Fito
- Zanga-zanga kan tsadar rayuwa da ake yi a Najeriya ta isa birnin Legas domin nuna adawa kan farashin kayayyaki ya yi tashin gwauron zabi
- Wasu mata da matasa ƴan kasuwa a yankin Ibeju-Lekki sun fito domin nuna adawa kan yadda rayuwa ke ci gaba da yin tsada
- Masu zanga-zangar sun riƙe kwalaye masu rubucen da ke tunatar da shugaban ƙasa Bola Tinubu cewa akwai yunwa a ƙasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - Al’ummar Legas sun bi sahun jihohin da aka gudanar da zanga-zangar nuna rashin gamsuwa da tsadar rayuwa a ƙasar nan.
A Legas, mata da matasa ƴan kasuwa sun yi zanga-zanga a unguwar Ibeju-Lekki da ke jihar Legas a ranar Asabar, 10 ga watan Fabrairu, cewar rahoton Daily Trust.
Sun ɗauki kwalaye masu rubuce-rubuce irin su “Baba Tinubu, ƴan Nijeriya suna jin yunwa” da ‘Tinubu, ka zo ka cece mu’ da dai sauransu, rahoton Vanguard ya tabbatar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zanga-zangar ita ce ta baya-bayan nan a jerin zanga-zangar da aka gudanar a jihohin Kogi da Osun da Neja da kuma Kano kan tsadar rayuwa a ƙasar nan.
Tun bayan cire tallafin man fetur a watan Mayun 2023, farashin kayan masarufi ya yi tashin gwauron zabi a ƙasar nan.
Wannan tsadar kayayyakin tare da faɗuwar darajar Naira ya sanya an shiga halin matsi a cikin Najeriya, inda mutane ke kokawa kan yadda rayuwa ta yi matuƙar tsada.
Sabuwar zanga-zanga ta ɓarke kan tsadar rayuwa
Labari ya zo cewa biyo bayan zanga-zangar da aka yi a jihar Neja kan tsadar rayuwa, wata sabuwar zanga-zangar ta sake ɓarkewa a birnin Suleja, na jihar Neja..
Masu zanga-zangar dai sun fito kan tituna domin nuna adawarsu kan yadda rayuwa ta yi tsada a ƙasar nan.
Masu zanga-zangar sun yi kira ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da ya kawo karshen wannan tsadar rayuwa saboda suna cikin wahala.
Ƴan Sanda Sun Cafke Masu Zanga-Zanga
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Neja ta cafke wasu mutum 25 kan jagorantar zanga-zanga a birnin na jihar Neja.
Rundunar ta tabbatar da cewa za ta tura su zuwa kotu da zarar kammala bincike kan tuhumar tayar da tarzoma a yayin zanga-zangar.
Asali: Legit.ng