“Rayuwa Babbar Kyauta Ce”: Sakon Karshe da Shugaban Bankin Access Ya Saki Kafin Hatsarin Jirgi
- Wani jirgi mai saukar ungulu dauke da Herbert Wigwe, shugaban bankin Access, ya yi hatsari a daren ranar Juma'a a US
- Mutane shida da ke cikin jirgin, wadanda suka hada da Wigwe, matarsa, dansa da Abimbola Ogunbanjo, tsohon shugaban NGX, duk sun mutu
- 'Yan kwanaki kafin mummunan hatsarin, Wigwe, attajirin miloniya, ya wallafa wasu sakonni a shafinsa na X game da rayuwa, iyali da sauransu
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Herbert Wigwe, marigayi shugaban bankin Access, ya kasance mai karafafa gwiwa ga 'yan Najeriya, har lokacin da yake gab da barin duniya.
A shafukansa na soshiyal midiya, marigayin yana yawan sanar da mabiyansa ayyukansa sannan ya kan karfafa masu gwiwa da yi masu zantuka masu dadi.
Herbert Wigwe ya kasance hamshakin biloniya
Kwanaki 21 kain mutuwarsa a hatsarin jirgi mai saukar ungulu yayin da yake kasar Amurka a ranar Juma'a, 9 ga watan fabrairu, Wigwe ya sake wallafa sakon karfafa gwiwa ga dubban mabiyansa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A shafinsa na X, @HerbertOWigwe, ya rubuta a ranar 19 ga watan Janairu:
"A yau da kullun, mu dunga tuna cewa rayuwa babbar kyauta ce - damar jan numfashi, jin tabi, so, kwarewa da sadarwa.
"Ya kamata mu girmama wannan kyauta ta hanyar yin rayuwa tare da manufa, alheri, da godiya, wanda ke sa kowani lokaci ya zama mai daraja. Mu dunga kidaya kwanakinmu."
Haka kuma, kwanaki biyu kafin mutuwarsa, a ranar Laraba, 7 ga watan Fabrairu, ya jinjinawa matan Afrika.
Ya rubuta:
"Mun lura kuma mun yaba da gagarumin tasirin da matan Afirka ke da shi yayin da suke share hanyar samar da kyakkyawar makoma ga kowanenmu.
"Na shafe lokuta masu ban mamaki tare da babbar jami'ar gudanarwa, Yvonne Victor-Olomu."
Yadda shugaban bakin Access ya mutu
A baya Legit Hausa ta rahoto cewa shugaban kamfanin Access Holdings, Herbert Wigwe ya yi hatsari a cikin jirgi mai saukan ungulu yayin da ya ke Amurka a ranar Juma'a.
A cewar rahotanni daban-daban, lamarin ya faru a California kusa da iyakar Nevada, inda Wigwe, ke tare da matarsa da dansa.
Asali: Legit.ng