Tsadar Rayuwa: Kotu Ta Tura Wani Tela Gidan Yari Kan 'Sace Tukunyar Miya'
- Tsadar rayuwa da ke adabar 'yan Najeriya biyo bayan tsare-tsaren gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta saka wani tela daukan mataki mara kyau
- Adua Fatogun, ya sace tukunyar miya a jihar Ondo kuma alkalin kotun Majistare da ke zamanta a Oke Eda a Akure, babban birnin jihar Ondo ya aike da shi gidan yari
- An zargi dan shekara 19, Fatogun, da laifin kutse da sata amma ya musanta hakan amma dai an bashi masauki a gidan yari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe
Jihar Ondo - A yayin da 'yan Najeriya ke fama da tsadar rayuwa, wata kotun majistare da ke zamanta a Oke Eda a Akure, babban birnin jihar Ondo ta bada umurnin tsare wani tela, Adua Fatogun, a gidan yari kan zarginsa da satar tukunya makil da miya.
Fatogun wanda ake daure a ranar Laraba, an ce ya aikata laifin ne a ranar 12 ga watan Oktoban 2023, misalin karfe 9 na safe a layin Ifeleye, Ayeyemi, birnin Ondo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kuma yi ce dan shekara 19 ya sace wasu kayayyaki mallakar Felix Ogunbolade, Adeqoga Aboodun da Akinsete da darajarsu ya kai N311,100.
Fatogun ya musanta zargin kutsawa cikin gida da sata da aka karanto masa kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto.
Sufetan 'yan sanda, Bernard Olagbayi, ya ce laifukan da ake zargin Fatogun sun ci karo da sashi na 383 kuma doka ta tanadi hukuncinsu a sashi na 412(1), 390(9) na kundin 'Criminal Code Cap 37, Volume 1, na Dokokin Jihar Ondo.
Sai dai, ya shawarci kotun ta dage cigaba da sauraron shari'ar domin ba shi damar shirya shaidunsa da zai gabatar.
Alkalin kotun na majistare, O.A. Omofolarin, ya bada umurnin a tsare wanda ake zargin a gidan gyaran hali ya kuma dage cigaba da shari'ar zuwa ranar 19 ga watan Fabrairun 2024.
Fitaccen Malamin Addini Ya Yi Hasashen Cewa Buhun Shinkafa Zai Kai N90,000
A wani rahoton a baya, kun ji cewa malamin addini Primate Elijah Ayodele, na cocin INRI, ya yi gagarumin gargadi ga Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Malamin ya bayyana cewa Najeriya za ta fuskanci durkushewar tattalin arziki muddin ba a dauki matakan gaggawa ba, Daily Post ta rahoto.
Ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Osho Oluwatosin mai taimaka masa a bangaren harkokin labarai.
Asali: Legit.ng