EFCC Ta Bankaɗo Sabuwar Badakalar Makudan Kudi Kan Tsohon Gwamnan CBN, Za Cafke Matarsa da Wasu 3
- Hukumar EFCC ta ayyana neman matar tsohon gwamnan babban bankin Najeriya ruwa a jallo tare da wasu mutum uku ranar Jumu'a
- A wani hoto da ta fitar, EFCC tana zarginsu da haɗa baki da Godwin Emefiele wajen wawure maƙudan kuɗaɗe daga asusun gwamnatin tarayya
- Ta roki ƴan Najeriya da su taimaka su bada bayanin inda za a kama waɗanda ake zargin domin ɗaukar matakin da ya dace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta ayyana neman Margaret Emefiele, matar tsohon gwamnan babban banki (CBN), Godwin Emefiele, ruwa a jallo.
Kamar yadda ta wallafa a manhajar X watau Twitter, EFCC ta ayyana neman matar Emefiele tare da wasu mutum uku ruwa a jallo ne kan karkatar da wasu maƙudan kuɗaɗe.
Waɗanda hukumar yaƙi da marasa gaskiya EFCC ta ayyana nema ruwa da jallon sune Misis Emefiele, Mista Eric Odoh, Anita Omoile da mijinta, Jonathan Omoile.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyaaa EFCC ke neman kama matar Emefiele?
Da daren jiya Jumu'a, 9 ga watan Fabrairu, EFCC ta ce ta ɗauki wannan matakin ne bisa zarginsu da haɗa baki tsohon gwamnan CBN wajen karkatar da kuɗin gwamnati.
EFCC ta ce tana zargin matar Emefiele, da mutum uku da haɗa baki da tsohon gwamnan, "wajen karkatar da kuɗin gwamnatin tarayya masu yawa zuwa aljihunsu."
Sauran laifukan da ake zarginsu da aikatawa sun haɗa da, "mallakar kuɗi ta hanyar ƙarya da satar dukiyar talakawa wanda ya saɓawa sashi na 411, 287, da 314 na kundin laifukan Legas."
Cikakken bayani kan laifukan hukumar EFCC ke zargin waɗannan mutane da aikatawa na ƙunshe a wani hoto da hukumar ta wallafa ranar Jumu'a da daddare.
A ƙarshe, EFCC ta roƙi duk wanda yake da bayanin wurin da waɗanda ake zargin suka buya ya garzaya ya bada rahoto ga ofishin hukumar ko caji ofis mafi kusa.
Tinubu da Gwamnoni 22 Zasu Tafi Kallon Wasan Ƙarshe
A wani rahoton kuma Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, zai je kallon wasan ƙarshe na gasar cin kofin AFCON wanda tawagar Super Eagles zata kara da Ivory Coast.
Ƴan wasan Najeriya na shirye-shiryen ɓarje gumi da masu masaukin baƙi ƙasar Ivory Coast a wasan karshe a gasar cin kofin nahiyar Afirka AFCON.
Asali: Legit.ng